Trump Na Batun Tattaunawa, Iran Ta Kai Hare Hare Masu Zafi kan Isra'ila

Trump Na Batun Tattaunawa, Iran Ta Kai Hare Hare Masu Zafi kan Isra'ila

  • Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), na ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka
  • IRGC ta sanar da cewa ta kai hare-hare kan wurare masu muhimmanci a Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka wajen kai hare-haren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ta sanar da ƙaddamar da rukuni na 78 na hare-haren ramuwar gayya na "Operation True Promise 4".

Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta kai harin ne kan muhimman wurare a Isra'ila kamar Dimona, Tel Aviv, da Eilat, gami da sansanonin sojojin Amurka da dama a yankin.

Kara karanta wannan

Iran ta yi iƙirarin kai harin bama bamai wasu sansanoni a UAE da Kuwait, ta fadi dalili

Iran ta harba makamai kan Isra'ila
Makami mai linzami na Iran da aka harba Hoto: @IRIran_Military
Source: Twitter

Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da IRGC ta fitar ranar Talata, 24 ga watan Maris 2025.

Rundunar IRGC ta bayyana wannan sabon mataki na farmakin a matsayin wani gagarumin ci gaba da ya haɗa da ruwan makamai masu linzami kan wuraren maƙiya.

IRGC ta kafa babban tarihi

Sanarwar ta nuna cewa wannan mataki na baya-bayan nan, "ya kafa wani babban tarihi a jerin abubuwan da suka faru a wannan yaƙin."

A cewar sanarwar, an farmaki wurare a tashar jiragen ruwa ta Eilat, da Dimona wani birni mai tsauraran matakan tsaro wanda ke kusa da sanannen wurin nukiliya na Isra'ila, da kuma Arewacin Tel Aviv, jaridar Al-Mayadeen English ta kawo labarin.

Wadanne makamai aka harba kan Isra'ila

Rundunar ta ce an kai farmakin ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami na Emad da Qadr masu kawuna da dama tare da jirage marasa matuƙa.

Kara karanta wannan

Ana cikin murnar Sallah, Iran ta shammaci Amurka da Isra'ila a sababbin hare hare

Wannan ne karo na biyu da rundunar ke farmakar Dimona, kwanaki kaɗan bayan harin farko na martani wanda ya girgiza yankunan sakamakon mace-mace da raunuka da suka shafi mutane 200 a birnin da kuma birnin Arad da ke kusa.

Rundunar IRGC ta ƙara da cewa an kuma kai hari kan sansanonin sojojin Amurka da dama a yankin a lokacin wannan farmaki karo na 78.

Iran na harba makamai masu linzami kan Isra'ila
Makami mai linzami na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hoto: @IRIran_Military
Source: Twitter

IRGC ta aika da gargadi

Sanarwar ta ci gaba da cewa rundunar IRGC tana tattaunawa da azzalumai masu kisan yara ta hanyar ayyukan soja masu tasiri.

Ta nuna cewa yawancin rukunonin yaƙi na IRGC, gami da miliyoyin dakarun sa-kai na Basij, har yanzu ba su shiga fagen fama ba, tana mai gargaɗin cewa shigar su na iya tsananta rikicin kuma ya jefa azzaluman cikin halin da ba za su iya tsira ba.

Trump ya magantu kan shiryawa da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan batun zama teburin sulhu da Iran.

Trump ya mika bukata ga gwamnatin Iran game da mallakar makamai masu linzami, inda ya ce hakan zai sanya samun zaman lafiya a tsakaninsu.

Shugaban kasar na Amurka ya bukaci Iran ta dakatar da shirinta na makamai masu linzami na tsawon shekaru biyar a matsayin sharadin samun zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng