Matsala Sabuwa: Babbar Matatar Man Amurka Ta Kama da Wuta ana Yaki da Iran
- Yayin da duniya ke fuskantar matsalar makamashi saboda yakin da ake da Iran, wata babbar matatar mai da ke Amurka ta kama da wuta
- Rahotanni sun bayyana cewa wuta ta tashi a matatar kamfanin makamashi na Valeromai mai iya tace gangar mai 380,000 a rana a Texas
- A halin yanzu, hukumomi na cigaba da tantance bayanai game da barnar da ake tunani gobarar ta haifar domin sanin matakan da za a dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Gobara ta girgiza wata babbar matatar mai a jihar Texas a Amurka, inda wuta ta tashi tare da hayaki mai yawa yana tashi sama.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne a daren Litinin a matatar mai da ke Port Arthur bayan fashewar wasu abubuwa da ke da alaka da wata na'ura.

Source: Getty Images
Rahoton Reuters ya nuna cewa Gobarar ta afku ne a matatar kamfanin makamashi na Valero mai iya tace gangar mai 380,000 a rana, daya daga cikin manyan cibiyoyin sarrafa mai a Amurka.
Wuta ta kama a matatar Amurka
Gobarar ta girgiza bangaren makamashi na Amurka, musamman a lokacin da farashin mai ke tashin gwauron zabi sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya.
An rufe matatar cikin gaggawa, yayin da hukumomi suka umarci mazauna yankin da su zauna a cikin gidajensu saboda hayaki baki mai kauri da ke mamaye sararin samaniyar gabashin Texas.
Jami’an agajin gaggawa sun bayar da umarnin kowa ya zauna a gida domin kare lafiyarsa. Hotuna daga wurin sun nuna harshen wuta mai tsayi da kuma hayaki baki mai yawa yana tashi sama.
Bayanin da matatar Amurka ta yi
Kamfanin Valero ya tabbatar da cewa gobara ta tashi a daya daga cikin sassan matatar, yana mai cewa an tantance dukkan ma’aikata kuma suna karkashin kulawa.
Rahoton WIO News ya bayyana cewa kamfanin ya jaddada cewa kare rayukan ma’aikata shi ne babban abin da ya fi ba da muhimmanci.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoton, ba a tabbatar da mutuwa ko jikkata ba. Sai dai mazauna yankin sun ce sun ji karar fashewa mai karfi wacce ta girgiza tagogi da gine-gine.
Har yanzu ba a gano musabbabin fashewar ba, kuma hukumomi ba su bayyana tsawon lokacin da za a ci gaba da umarnin zama a gida ba.

Source: Getty Images
Matatar Port Arthur na daya daga cikin mafi girma a Amurka, tana sarrafa danyen mai zuwa fetur, dizel da man jirgin sama. Tana da karfin sarrafa kusan gangar mai 435,000 a rana, tare da daukar kusan ma’aikata 800.
Ga bidiyon matatar da Brian Allen ya wallafa a X:
Jirgin sama ya yi hadari a Amurka
A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin Canada ya yi hadari yayin da ya zo sauka a wani filin tashi da saukar jirage a kasar Amurka.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar hadarin yayin da hukumar kashe gobara ta bayyana makatan gaggawa da ta dauka.
Hukumar kula da tashin jirage a Amurka ta sanar da cewa an dakatar da aiki da filin jirgin zuwa wani lokaci domin samun damar daidaita lamura.
Asali: Legit.ng

