Wata Sabuwa: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Shirin da Ta Yi a kan Trump

Wata Sabuwa: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Shirin da Ta Yi a kan Trump

  • Yakin da ake yi tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da daukar zafi a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Babban kwamanda a sojojin Iran, Manjo Janar Ali Abdollahi, ya bayyana cewa akwai tanadin da suka yi kan shugaban kasar Amurka, Donald Trump
  • Manjo Janar Ali Abdollahi ya bayyana cewa Trump da Isra'ila za su ga abubuwan ban mamaki da aka shirya musu

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Wani babban kwamandan sojojin Iran, Manjo Janar Ali Abdollahi, ya yi magana kan yakin da ake ci gaba da yi tsakanin kasarsa, Amurka da Isra'ila.

Manjo Janar Ali Abdollahi ya ce Jamhuriyar Musulunci tana da abubuwan mamaki da ta tanada ga Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke ci gaba da yin barazanar baki ga ƙasar, da kuma gwamnatin Isra'ila.

Kara karanta wannan

Bayan kashe manyan jagorori 2 a Iran, Isra'ila ta fadi shirinta kan Mojtaba Khamenei

Iran ta shiryawa Donald Trump abin mamaki
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Tashar Press tv ta kasar Iran ta kawo rahoto kan maganganun da babban kwamandan ya yi a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.

Wane tanadi Iran ta yi wa Trump?

Manjo Janar Ali Abdollahi, shi ne kwamandan babban helkwatar Khatam al-Anbiya, wadda ita ce babbar rundunar gudanarwa ta Iran da ke daidaita ayyuka tsakanin rundunar sojoji da dakarun IRGC.

“Mun riga mun bayyana cewa Trump, shugaban Amurka, yana ta fitar da gargaɗi ta hanyar baki, amma dole ne ya sani cewa rundunonin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna da abubuwan mamaki da suka tanada gare shi da kuma gwamnatin Isra'ila a matsayin wakiliyarsa kuma mai biyayya gare shi."
"A yau, misali ɗaya na waɗannan shi ne harbin jirgin yaƙi na zamani samfurin F-35. Su sa rai ga ƙarin abubuwan mamaki.”

- Manjo Janar Ali Abdollahi

Iran na ci gaba da kai hare-hare

Waɗannan kalaman sun zo ne a daidai lokacin da rundunonin sojojin ke ci gaba da fafatawa a harin ramuwar gayya na 'Operation True Promise 4', wanda ya fara jim kaɗan bayan harin baya-bayan nan na Washington da Tel Aviv a kan Jamhuriyar Musulunci a karshen watan jiya.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Sansanonin Amurka a duk faɗin yankin, ciki har da waɗanda ke Qatar, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Kuwait, da Saudi Arabia, sun fuskanci gagarumar ramuwar gayya.

Harin ramuwar gayyar ya kuma shafi wurare masu muhimmanci da na dabarun yaƙi a Isra'ila, ciki har da waɗanda ke birnin Tel Aviv, birni mai tsarki na al-Quds, tashar jirgin ruwa ta Haifa, Be’er Sheva, wadda ita ce cibiyar fasahar gwamnatin da kuma hamadar Negev.

Iran ta kai hari kan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta kaddamar da sabon harin ramuwar gayya kan Isra'ila.

Rundunar IRGC ta kai hari kan matatun man fetur na Isra'ila tare da gabatar da sabon makamin linzami mai cin dogon zango da ake kira “Nasrallah” wanda ke ɗauke da bama-bamai masu yawa.

IRGC ta ce sabon harin ya nufi matatun man fetur na Ashdod da Haifa, waɗanda ke cikin manyan matatun gwamnatin Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng