"Ba za a ga Watan Shawwal da Idanu ba": Masani Ya Yi Magana ana Shirin Sallah
- Wani fitaccen masani kuma mai ilimin taurari, Simwal Usman Jibril ya bayyana cewa duk da cewa an cika azumi 30, ba za a ga watan Shawwal ba
- Ya bayyana cewa zai yi wahala a iya ganin fitowar jinjirin wata ba a Najeriya, inda ya yi magana a kan wadanda suka ce sun ga wata a Nijar
- Simwal ya bayyana abubuwan da za su hana jama'a su iya ganin watan da idanunsu, duk kuwa da cewa tabbas sabon wata na Sallah ya kama
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – Wani masani kan ilimin taurari, Simwal Usman Jibril ya bayyana cewa ba zai yiwu a ga jinjirin watan yau da ido a Najeriya ba.
Ya bayyana haka ne a yayin da ya ce ya san yanzu haka jama'a suna ta shirin fita kallon wata yayin da ake 'dokin Sallah karama.

Source: Twitter
Simwal ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yayin da jama'a suke cika azumi 30 a wannan shekara.
Abin da zai hana ganin watan Shawwal
Simwal Usman Jibril ya ce duk da cewa an saba samun muhawara a duk shekara game da sahihancin ganin jinjirin wata, wannan karon lissafin kimiyya ya nuna karara cewa ganin sa ba zai yiwu ba.
A cewarsa, shekarun watan a yau sun kai kusan sa’o’i 16 kacal bayan haihuwarsa, alhali mafi yawan lokuta, jinjirin watan kan fara bayyana a sarari ne idan ya kai akalla sa’o’i 18 zuwa sama.

Source: Facebook
Wannan yana nufin cewa har yanzu watan bai kai matakin da za a iya hango shi da ido ba, musamman a yankunan Najeriya.
Simwal ya kara da cewa hasken jinjirin watan bai wuce 0.5% ba, wanda ke nuni da cewa hasken ya yi rauni matuƙa.
Wannan ƙarancin haske yana daga cikin manyan dalilan da ke hana ganin jinjiri, ko da kuwa ana amfani da wasu na’urori masu kara karfin gani.
Simwal ya magantu kan ganin Shawwal a Nijar
Har ila yau, ya ƙara da cewa ko a ƙasashe makwabta irin su Nijar da Mali, inda aka ruwaito an ga jinjirin jiya, ba zai yiwu a sake ganinsa yau ba bisa ƙa’idar ilimin taurari.
Sai dai ya kwantar da hankulan al’umma da cewa akwai kyakkyawan fata cewa gobe Juma’a20 ga watan Maris, 2025 za a iya ganin jinjirin watan a cikin sauƙi In sha Allah.
A cewarsa, zuwa lokacin faduwar rana gobe, watan zai kai kimanin sa’o’i 40 da haihuwa, wanda hakan ya wuce ƙa’idar da ake buƙata domin ganinsa da ido muraran.
Ya bayyana cewa wannan yanayi yana cikin tsarin da Allah Maddaukakin Sarki Ya tsara tun asali, inda motsin rana da wata ke tafiya bisa ƙayyadadden lissafi mai inganci.
Ya kawo hujja da ayar Al-Qur’ani mai girma daga Suratul Rahman (55:5) wacce ke cewa:
“Rana da wata suna tafiya bisa lissafi madaidaici.”
Ba a ga wata ba - Sarkin Musulmi
A wani labarin kun ji cewa Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa ba ta samu rahoton ganin jinjirin watan karamar Sallah ba a fadin Najeriya, saboda haka akwai saura.
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bayyana cewa za a cika azumi 30, sannan a yi sallar idi ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026 da yardar Allah.
Ya kuma taya al'ummar musulmi murnar zagayowar karamar Sallah, inda ya bukaci su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Najeriya addu'a na samun ci gaba mai dore wa.
Asali: Legit.ng


