Kasashe 5 da Suka Kira Iran Ta Waya, Suka Nuna ana Tare bayan Fara Yaki da Amurka

Kasashe 5 da Suka Kira Iran Ta Waya, Suka Nuna ana Tare bayan Fara Yaki da Amurka

Tun bayan fara yakin Amurka/Isra'ila da Iran a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, kasashe da dama sun kiraTehran a wayar tarho.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - A ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 yaki ya barke a Gabas ta Tsakiya bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a Iran.

Lamarin ya jawo asarar rayuka, lalata dukiyoyi da jefa duniya cikin matsalar makamashi, wanda hakan ya sa kasashen duniya tattaunawa da Iran.

Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian
Shugaba Massoud Pezeshkian yana magana a taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin kasashen duniya da suka yi magana da Iran ta waya domin tattauna hanyoyin da za a kawo karshen yakin.

1. Faransa ta kira Iran a waya

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya tattauna da Iran ta waya domin ganin an samu mafita a yakin da ake a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Iran ta yi luguden wuta yayin da Larabawa ke tsaka da taro a Saudiyya

A wani sako da ya wallafa a X, Macron ya ce:

"Na yi magana kai tsaye da shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian."
"Na bukace shi da ya kawo karshen hare-haren da Iran ke kaiwa kasashen yankin, wadanda ba za a amince da su ba, ko dai kai tsaye ko ta hannun wakilai, ciki har da a Lebanon da Iraki.
Emmanuel Macron na waya
Shugaban Faransa yayi wayar tarho. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kara da cewa:

"Karin tsanantar rikicin da ake gani ba tare da takaita shi ba yana jefa daukacin yankin cikin rudani, tare da manyan illoli a yau da kuma a shekaru masu zuwa."

2. Putin ya kira Mojtaba Khamenei

Firaministan kasar Rasha, Vladimir Putin ya tattauna da kasar Iran a lokuta daban-daban tun bayan fara yaki da Amurka/Isra'ila suka yi.

Bayan kisan Ali Larijani, rahoton Anadolu ya rahoto Putin ya ce:

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu kan rasuwar sakataren majalisar tsaron kasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ali Larijani,”
Shugaba Valadimir Putin yana waya
Firaministan Rasha, Valadimir Putin yana waya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Putin ya bayyana Larijani a matsayin “aboki na gaskiya” ga Rasha, yana mai cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwar dabarun hadaka tsakanin Moscow da Tehran.

Kara karanta wannan

China ta shirya kai dauki, ta bayyana tallafin da za ta tura kasar Musulunci ta Iran

3. Pakistan ta yi magana da Iran

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, domin tattauna yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta.

A yayin kiran, shugabannin biyu sun tattauna rikicin da ke gudana wanda ya hada da Amurka da Isra’ila, tare da jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Samaa TV ya nuna cewa Firaministan Pakistan din ya kuma mika ta’aziyyarsa kan shahadar Ayatollah Khamenei tare da taya sabon Jagoran kasar murna.

4. India ta yi magana da Iran ta waya

Kamar sauran kasashe, Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian.

Firaministan Indiya, Narendra Modi
Firaminista Narendra Modi na duba waya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Iran International ya nuna cewa inda Modi ya yi magana kan tsaron ‘yan kasar Indiya da kuma tabbatar da ci gaba da zirga-zirgar kayayyaki da makamashi ba tare da tangarda ba yayin tattaunawar.

5. Azerbaijan ta yi magana da Iran

Kara karanta wannan

"Ba mu miƙa wuya ga azzalumai": Iran ta gindaya sharadin kawo ƙarshen yaƙi da Amurka

A ranar 8 ga Maris, Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Jamhuriyar Azerbaijan, Ilham Aliyev.

Pezeshkian ya yi godiya ga shugaba Aliyev bisa ziyarar da ya kai ofishin jakadancin Iran da ke Azerbaijan domin mika ta’aziyya kan rasuwar Jagoran koli na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Shugaban Jamhuriyar Azerbaijan, Ilham Aliyev.
Shugaban Jamhuriyar Azerbaijan, Ilham Aliyev yana waya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin kasar ta wallafa cewa shugaba Ilham Aliyev ya sake bayyana ta’aziyyarsa kan mutuwar fararen hula da dama a abubuwan da suka faru a Iran.

Larabawa sun yi taro a Saudiyya

A wani labarin, mun kawo muku cewa ministocin kasashen Musulmi da Larabawa sun yi wani taron gaggawa a kasar Saudiyya.

Rahoto ya nuna cewa sun gudanar da taron ne a ranar Laraba, 18 ga watan Maris a birnin Riyadh domin tattauna matsalar tsaro.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana cewa taron zai mayar da hankali game da yakin da ake tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng