Yakin Iran: An Hango Bakin Jiragen Yaki a Amurka, a Saman Jami'an Trump
- An hango wasu bakin jirage a wani sansanin sojin Amurka da ke birnin Washington, inda manyan jami'an Donald Trump ke zama
- Ministan yaki da na kasashen wajen Amurka na cikin manyan jami'an da suke zama a sansanin da aka hango jirage marasa matuka
- Hakan na zuwa ne yayin da ake tsaka da gwabzawa a fagen fama tsakanin sojojin Amurka/Isra'ila da Iran a yakin da ake a Gabas ta tsakiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - An samu rudani bayan bayyanar wasu jirage marasa matuka a Amurka yayin da ake cigaba da yaki da Iran a Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu manyan jami'an gwamnati suka bayyana dalilan kin yin karin haske.

Source: Getty Images
Rahoton Washington Post ya nuna cewa an hango jiragen yakin ne a kusa da wani waje da manyan jami'an gwamnatin Trump ke zaune.
Jirgin da aka hango a Amurka
Jami’an Amurka sun gano jiragen yaki marasa matuka a saman wani sansanin sojoji da ke Washington inda ministan harkokin wajen kasar, Marco Rubio, da ministan yaki, Pete Hegseth, ke zaune.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Laraba lamarin ya faru, wasu mutane uku da aka sanar da su halin da ake ciki ne suka fitar da labarin.

Source: Getty Images
Rahoton ya ce jami’an ba su iya tantance inda jiragen marasa matukin suka fito ba, yana mai ambaton mutane biyu daga cikin wadanda aka sanar.
Matakin da Amurka ke shirin dauka
An ce jiragen da aka gani a saman Fort McNair sun sa jami’ai suka fara tunanin ko za a sauya wa Rubio da Hegseth wurin zama, in ji rahoton.
Sai dai rahoton ya kara da cewa har yanzu ministocin ba su tashi daga wuraren zamansu ba, yana mai nuni da wani babban jami’i a gwamnati da ya sanar da hakan.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka
Jaridar ta ce rundunar sojin Amurka na sa ido sosai kan yiwuwar barazana sakamakon karin matakin tsaro da aka dauka bisa yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.
Bincike da masana suka kara
A kokarin tantance abin da ya faru, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa cewa bai samu damar tabbatar da rahoton kai tsaye ba.
Ma'aikatar yaki da ke Pentagon da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ba su mayar da martani ba kan bukatar yin tsokaci da aka musu.
Babban mai magana da yawun Pentagon, Sean Parnell, ya ki yin karin bayani kan lamarin jiragen marasa matuka da aka tambaye shi saboda dalilan tsaro.
Iran ta yi luguden wuta a Saudi
A wani labarin, kun ji cewa Ira ta harba makamai masu linzami zuwa birnin Riyadh na Saudiyya yayin da kasashen Larabawa ke taro.
Kasashen Larabawa da na Musulmi sun hadu a Saudiyya ranar Laraba domin tattauna batun yakin da ake Gabas ta Tsakiya.
Suna tsaka da taron ne suka rika jin karar saukar makaman Iran, abin da ya sa Saudiyya cewa ba za ta lamunci haka ba sam.
Asali: Legit.ng
