Bayan Gama Duban Jinjirin Wata, Kasar Saudiyya Ta Sanar da Ranar Karamar Sallah

Bayan Gama Duban Jinjirin Wata, Kasar Saudiyya Ta Sanar da Ranar Karamar Sallah

  • Saudiyya ta kammala tattara bayanai daga duka cibiyoyin da ake zuwa duban jinjirin wata, kuma ta tabbatar da cewa ba a samu ganin shi na
  • Bisa haka, hukumomin Saudiyya suka sanar da cewa musulmi za su cika azumi 30, sannan za a yi idin karamar Sallah ranar Juma'a, 20 ga Maris, 2026
  • Tun farko, bayanai sun nuna cewa an samu gajimare a sararin samaniya a wasu wuraren duban wata na kasar Saudiyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Rahotanni daga Saudiyya sun nuna cewa an kammala aikin duban jinjirin watan Shawwal, wata na 10 a kalandar addinin Musulunci.

Saudiyya ta tabbatar da cewa ba a samu sahiihin rahoton ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1447AH ba a yau Laraba, 29 ga watan Ramadan, wanda ya zo daidai da 18 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

29 ko 30: Malamin addini ya riga sarkin Musulmi, ya sanar da ranar karamar Sallah a Najeriya

Duban wata.
Na'urorin da ake amfani da su wajen duba jinjirin wata a Saudiyya Hoto: @Haramain
Source: Twitter

Ba a ga watan Sallah a Saudiyya ba

Hakan na kunshe ne a sanarwar da hukumar kula da masallacin Harami da Masallacin Annabi SAW, ta wallafa a shafinta na X, Haramain, yau Laraba.

Bisa haka, masarautar Saudiyya ta bayyana cewa musulmi za su cika azumi 30 cif a wannan shekara, tare da ayyana ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranar karamar Sallah.

Saudiyya ta sanar da ranar karamar Sallah

Sanarwar ta ce:

"Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ƙasar Saudi Arabia. Saboda haka, za a yi idin karamar Sallah a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026, wanda zai zama 1 ga Shawwal, 1447AH."
"Allah Ya ba mu ikon amfani da sauran lokutan da suka rage na wannan wata mai albarka wajen ayyukan da za su faranta masa rai.
"Allah Ya karɓi azumin mu, tsayuwar dararen mu, da sauran ayyukan mu na ƙwarai, sannan Ya sa mu ga wasu watannin Ramadan masu yawa cikin ƙoshin lafiya. Ameen."

Kara karanta wannan

Oman ta saba wa Saudiyya da Najeriya, ta fitar da sanarwa kan watan karamar Sallah

Yadda aka duba watan Sallah a Saudiyya

Tun farko, rahotanni sun nuna cewa ba samu yanayi mai iyau ba a galibin wuraren da ake zuwa duban jinjirin wata a kasar Saudiyya.

A Al-Hariq, bayanai sun nuna cewa yanayin sararin samaniya ba shi da kyau tun farkoo, don haka ganin jinjirin watan Sallah na iya yin wahala.

Masu duban wata.
Masu duban jinjirin wata a kasar Saudiyya Hoto: @Haramain
Source: Twitter

Haka zalika a an samu gajimare a sararin samaniyar cibiyar duban wata ta Sudair, wanda hakan na iya sa ganin jinjirin watan Shawwal ya yi wahala.

Bayan kammala tattara bayanai daga kowace cibiya, kasar Saudiyya ta sanar da ranar Juma'a a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal, 1447AH, ma'ana ranar Karamar Sallah ta bana.

Za a fara duban watan Sallah a Oman

A wani labarin, kun ji cewa Oman ta nemi al'ummmar musulmin kasar su fara duban jinjirin watan karamar Sallah watau Shawwal, 1447AH daga ranar Alhamis mai zuwa.

Oman na daya daga cikin kasashen da suka fara azumi a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu, 2026, ma'ana dai ba su fara azumi rana daya da Saudiyya da Najeriya ba.

Hukumomin Oman sun bukaci ‘yan kasa da mazauna kasar da su rika sa ido domin neman ganin jinjirin watan, tare da kai rahoton ga kwamitocin da suka dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262