Dubu Ta Cika: Iran Ta Cafke Masu Taimakon Amurka da Isra'ila a Yakin da Ake Yi
- Mahukunta a Iran sun tabbatar da cafke daruruwan mutane da ake zargi da cin amanar kasa ta hanyar wasu ayyukan da suke yi
- Hakazalika, mahukuntan sun bayyana cewa za su ci gaba da cafke mutanen da ke marawa muradun Amurka da Isra'ila baya
- Hukumar leken asiri ta bayyana cewa an samu makamai a hannun cikin mutanen da aka cafke, tare da yin kira ga jama'a su kai rahoton duk abin da ba su yarda da shi ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Hukumomin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sanar da cafke karin daruruwan mutane a faɗin ƙasar.
Hakazalika sun sanar da gudanar da ayyukan kakkabe mutanen da suka bayyana a matsayin “maci amana” waɗanda ke mara wa muradun Amurka da Isra'ila baya.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa ma'aikatar leken asiri ta bayyana cafke mutanen a cikin wata sanarwa.
Mahukunta a Iran sun cafke wadanda ake zargi
Ta bayyana cewa an dakatar da ayyukan "ƙungiyoyin masu goyon bayan masarauta” guda 111 a cikin larduna 26 daga cikin 31 na Iran a daren Talata zuwa ranar Laraba, 17 ga watan Maris 2026.
An bayyana cewa mutanen da aka kama suna shirin kaddamar da ayyukan nuna adawa da tsarin mulkin addini na ƙasar wanda ya kifar da masarautar da Amurka ke goyon baya a juyin juya halin Musulunci na 1979.
An gudanar da bikin Nowruz a Iran
Al'ummar Iran sun shafe shekaru dubbai suna gudanar da bikin wuta da ake kira Chaharshanbe Suri a daren Larabar ƙarshe ta kowace shekara, domin maraba da sabuwar shekarar Farisa wato Nowruz.
Sai dai a wannan shekarar, hukumomi sun buƙaci masu goyon bayan gwamnati da su fito kan tituna don tabbatar da iko, yayin da jami'an tsaro ke kama duk wani mai adawa, a daidai lokacin da ake tsaka da yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran.

Kara karanta wannan
Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa
An gano makamai a hannun wadanda ake zargi
Ma'aikatar ta yi ikirarin cewa an gano wasu makamai a hannun mutanen da aka kama, sannan ta sabunta kiran ta ga jama'a da su kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba, tashar Iranpress ta kawo labarin.
Wasu daga cikin daruruwan da aka kama a birnin Karaj da ke kusa da Tehran sun “ƙona hotunan tsohon jagoran addini da aka kashe tare da yi masa batanci,” wato Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a farkon yaƙin ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Tun daga wannan lokacin ne aka zaɓi ɗan Khamenei, Mojtaba Khamenei, a matsayin sabon jagoran addini na Iran.

Source: Twitter
Amurka da Iran na son sauya gwamnati
Amurka da Isra'ila, waɗanda suka ayyana kifar da gwamnatin Iran a matsayin ɗaya daga cikin manufofinsu, sun kasance suna farmakar tsarin tsaron cikin gida na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).
Shingayen bincike na dakarun Basij sun kasance suna shan luguden wuta daga jirage marasa matuƙa tsawon mako guda, yayin da aka tabbatar da kisan shugaban tsaro Ali Larijani a daren jiya, tare da wani babban mataimaki a majalisar tsaro ta kasa.
Isra'ila ta sha alwashin kashe Mojtaba Khamenei
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta sha alwashin ganin bayan sabon jagoran addini na Iran.
Rundunar IDF ta bayyana cewa za ta farauto tare da kashe sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei a duk inda yake.
Hakazalika, rundunar ta bayyana cewa za ta ci gaba da farmakar jami'an gwamnatin Iran har ta ga bayansu.
Asali: Legit.ng

