Trump yi barazanar sake kai hari Tsibirin Kharg a Iran “don nishadi”

Trump yi barazanar sake kai hari Tsibirin Kharg a Iran “don nishadi”

  • Trump ya ce Amurka na iya sake kai hari tsibirin Kharg Island na Iran ba don komai ba sai don nishadi kawai
  • Ya ce hare-haren Amurka sun riga sun lalata yawancin wuraren sojin tsibirin tun bayan fara farmakar kasar Islama ta Iran
  • Shugaban Amurka ya ce sharuddan yarjejeniya da Iran ba su gamsar ba, dole a ci gaba da kai ruwa rana tsakaninsu

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Amurka na iya sake kai hari kan muhimmiyar cibiyar fitar da mai ta Iran da ke Kharg Island “don nishadi”, yayin da rikici ke ci gaba tsakanin Amurka da Iran.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da NBC News, inda ya ce hare-haren da sojojin Amurka suka kai sun riga sun lalata yawancin wuraren soji da ke tsibirin.

Trump zai sake kai hari Iran
Iran ya ce zai iya sake kai hari Iran | Hoto: Roberto Schmidt
Source: Getty Images

Ya ce:

“Mun riga mun lalata shi gaba daya. Amma kamar yadda kuka sani, ban kai hari kan layukan makamashi ba, domin sake gina su zai dauki shekaru.”

Kara karanta wannan

Harin tsibirin Kharg: Shugaban Amurka ya ga abin da bai yi tsammani ba a yaki da Iran

Sai dai Trump ya kara da cewa Amurka na iya sake kai wasu hare-hare kan tsibirin.

Ya ce sojojin Amurka na iya kai hari a wurin “sau biyu ko fiye… kawai don nishadi.”

Trump ya yi watsi da yarjejeniya da Iran

A yayin hirar, Trump ya kuma rage fata kan yiwuwar cimma yarjejeniya cikin gaggawa tsakanin Amurka da Iran.

Ya ce sharuddan da Iran ke gabatarwa ba su gamsar da Amurka ba.

A cewarsa:

“Sharuddan ba su kai matsayin da ake bukata ba tukuna.”

Muhimmancin tsibirin Kharg

Tsibirin Kharg na daya daga cikin wurare mafi muhimmanci wajen fitar da man fetur na Iran, inda ake jigilar mafi yawan man kasar zuwa kasuwannin duniya.

Tsibirin yana taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Iran, domin kusan 90% na man fetur da kasar ke fitarwa yana wucewa be ta wurin.

Hare-haren da Amurka ta kai a tsibirin na cikin yakin da ya fara a ranar 28 ga Fabrairu tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, wanda ya janyo tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana cikin gwabza fada, Trump ya fadi bukatar da shugabannin Iran suka nema

Har ila yau, rikicin ya shafi zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin ruwa ta Strait of Hormuz, wacce muhimmiyar hanya ce da ake jigilar kusan kaso mai yawa na man fetur na duniya.

A halin yanzu, kasashe da dama na ci gaba da fuskantar tsadar man fetur, ciki har da Najeriya da sauran kasashen duniya da suka dogara da shigo da man fetur.

Jiragen da Amurka ta saya don yakar Iran

A wani labarin, Sojojin Amurka sun tura jirage marasa matuƙi da ke kado makamai guda 10,000 da aka ƙera a Ukraine zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Amurka ta tura jiragen ne domin dakile hare-haren Iran ba tare da kashe kuɗi masu yawa kan makamai masu linzami ba. Wannan bayani ya fito ne daga sakataren rundunar sojin Amurka, Dan Driscoll.

A wata hira da ya yi, Driscoll ya bayyana cewa jirage marasa matuƙi na Merops, waɗanda ke amfani da fasahar basirar AI, an aika da su ne cikin kwanaki biyar bayan fara farmakin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng