Amurka ta Aika Jirage Marasa Matuƙi 10,000 Zuwa Gabas ta Tsakiya Don Dakile Hare Haren Iran
- Sojojin Amurka sun tura jirage marasa matuƙi da ke kado makamai guda 10,000 zuwa Gabas ta Tsakiya
- An ƙera jiragen Merops a Ukraine kuma suna amfani da fasahar AI wajen gudanar ayyukan yaki cikin sauki
- Ana sa ran za su rage amfani da makamai masu tsada kamar Patriot da THAAD da Amurka ke harbawa kan Iran
Amurka - Sojojin Amurka sun tura jirage marasa matuƙi da ke kado makamai guda 10,000 da aka ƙera a Ukraine zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta tura jiragen ne domin dakile hare-haren Iran ba tare da kashe kuɗi masu yawa kan makamai masu linzami ba. Wannan bayani ya fito ne daga sakataren rundunar sojin Amurka, Dan Driscoll.
A wata hira da ya yi, Driscoll ya bayyana cewa jirage marasa matuƙi na Merops, waɗanda ke amfani da fasahar basirar AI, an aika da su ne cikin kwanaki biyar bayan fara farmakin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Source: Getty Images
Kamfanin tsaro mai suna Project Eagle ne ya ƙera jiragen Merops, wanda tsohon shugaban kamfanin Google, Eric Schmidt, ke tallafawa. An fara tura waɗannan jirage marasa matuƙi zuwa Ukraine tun shekarar 2024.
Nawa ne kudin kowanne jirgi?
Driscoll ya ce kowanne jirgin Merops yana kai kusan $14,000 zuwa $15,000, amma idan aka saye su da yawa farashin na iya raguwa zuwa $3,000 zuwa $5,000 ga kowane jirgi mai kado makamai, rahoton Bloomberg.
Ya kara da cewa wannan ya fi arha idan aka kwatanta da jirage marasa matuƙi na Shahed na Iran, waɗanda farashinsu bai gaza $20,000 ba, kuma Iran na amfani da su sosai wajen kai hari kan Amurka da abokan kawancenta a yankin.
Driscoll ya ce:
“A zahiri mun fi fa’idantuwa a bangaren farashi. Duk lokacin da Iran ta harba ɗaya daga cikin waɗannan jirage marasa matuƙi kuma muka samu damar kakkabe shi, suna asarar kuɗi mai yawa.”
Yadda aka amfani a wadannan sabbin jirage
Amfani da makaman da aka gwada a yakin Rasha da Ukraine ya zo ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ba ta bukatar taimakon Ukraine wajen yakar jirage marasa matuƙi na Iran.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya taba ba da shawarar a tura taimako zuwa Gabas ta Tsakiya domin taimakawa wajen harbo jirage marasa matuƙi.
Sai dai Trump ya ce Amurka ba ta bukatar irin wannan taimako, kamar yadda ya bayyana wasu batutuwansana baya.
Ya ce a wata hira da Fox News Radio tare da Brian Kilmeade:
“A’a, ba mu bukatar taimakonsu wajen kariya daga jirage marasa matuƙi. Mun fi kowa sanin yadda ake sarrafa jirage marasa matuƙi. A gaskiya ma muna da mafi kyawun jirage marasa matuƙi a duniya.”
Idan aka fara amfani da jiragen Merops sosai, hakan na iya sauya tsarin kariyar sojojin Amurka da Isra’ila, waɗanda a baya suka dogara da tsarin kariya na Patriot da THAAD.

Kara karanta wannan
Magana ta Fito: Barnar da bama baman Iran suka yi wa sojojin Amurka bayan kai hari
Kashe kudin Amurka zai ragu
Amfani da makaman Merops rage kashe kudin Amurka da Isra’ila a yakin, inda makamansu ke kaiwa fiye da $4m kowanne, yayin da ake amfani da su wajen harbo jirage marasa matuƙi da makamai masu linzami na Iran masu arahan gaske.
Amurka kuma na ci gaba da tura wasu kayan karbo jirage marasa matuƙi zuwa yankin, ciki har da jirgin Coyote na kamfanin RTX Corp.

Source: Getty Images
Bugu da ƙari, rundunar sojin Amurka ta kuma tura jiragen Bumblebee, waɗanda aka ɗora musu bama-bamai domin bin sawun jirage marasa matuƙi na abokan gaba su yi karo da su su lalata su.
Su wa suka kera Bumblebee?
Kamfanin Perennial Autonomy ne ya ƙera tsarin Bumblebee, kuma an gwada shi a Ukraine, amma tun da farko an ƙirƙire shi ne domin kai hari kan abubuwa masu motsi.
Sojojin Amurka sun sayi tsarin Bumblebee ne ta wata yarjejeniya mai darajar $5.2m a watan Janairun 2026, ta hannun sabuwar rundunar Pentagon mai suna Joint Interagency Task Force 401.

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
An kafa wannan runduna ne domin haɓakawa da sayen kayayyakin kariya daga jirage marasa matuƙi, tare da gaggauta tura su ga rundunar soji.
Asali: Legit.ng

