Babbar Magana: An Yi Yunkurin Sasanta Amurka da Iran, Sakamakon Bai Yiwa Kasashe Dadi ba

Babbar Magana: An Yi Yunkurin Sasanta Amurka da Iran, Sakamakon Bai Yiwa Kasashe Dadi ba

Amurka - Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ƙasar Amurka ta yi watsi da yunƙurin wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya na fara tattaunawar diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Rahotanni daga majiyoyi masu masaniya kan tattaunawar sun ce ƙasashe da dama sun yi ƙoƙarin shiga tsakani domin tsagaita wuta, amma gwamnatin Trump ta nuna cewa ba zai yiwu ba a yanzu.

Amurka.
Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump Hoto: Anadolu
Source: Twitter

Iran ta ƙi yarda da sulhu da Amurka

A bangaren Tehran, majiyoyi biyu daga cikin manyan jami’an Iran sun shaidawa Reauters cewa ƙasar ba za ta amince da batun tsagaita wuta ba har sai Amurka da Isra’ila sun dakatar da duk hare-haren da suke kaiwa.

Iran ta kuma gabatar da wasu sharuɗɗa kafin ta amince da sulhu, ciki har da dakatar da hare-haren Amurka da Isra’ila gaba ɗaya da biyan diyya kn asarar da yakin ya haifar.

Yunƙurin sasanci daga wasu ƙasashe

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya faɗi dalilin da ya sa ƴan ta'adda suka fi kai hare hare a Ramadan

Ƙasashen da suka yi ƙoƙarin shiga tsakani sun haɗa da Oman, wacce ta taba shiga tsakani a tattaunawar Iran da Amurka kafin yaƙin, da Egypt, wacce ita ma ta yi ƙoƙarin sake buɗe zaman tattaunawa.

Sai dai majiyoyi sun ce Fadar White House ta bayyana cewa Shugaba Trump yana so ya ci gaba da hare-hare domin ƙara raunana ƙarfin sojojin Iran.

Wani jami’i a gwamnatin Amurka ya ce:

“Shugaban kasa ba ya sha’awar tattaunawa a yanzu. Za mu ci gaba da wannan yakin ba tare da tsayawa ba.”

An fara matsin lamba ga Trump

Wasu jami’an Amurka na gargadin cewa tsawon lokacin da za a dauka a yaƙin na iya jefa gwamnatin Trump cikin matsin lamba na siyasa, musamman saboda tashin farashin mai da fetur da karatowar zaɓukan majalisar dokokin Amurka.

Sai dai wasu masu ba shi shawara suna ƙarfafa shi da ya ci gaba da yaƙin domin lalata shirin makamai masu linzami na Iran da hana ta samun makamin nukiliya.

Duk da yunƙurin sasanci daga wasu ƙasashe, bangarorin biyu na ƙara tsaurara matsayinsu, lamarin da ke nuna cewa yaƙin na iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a samu mafita.

Ku saurari karin bayani...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262