To Fa: Musayar Wutar da Ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran Ta Shiga Wani Muhimmin Mataki
- Gwamnatin Isra'ila ta bayyana cewa a halin yanzu, yakin da take yi da kasar Iran ya shiga wani muhimmin mataki, wanda zai iya zama na karshe
- Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ne ya bayyana hakan, inda ya yaba da harin da Amurka ta kai kan kadarorin man feturin Iran
- Duk da karfin hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai wa, Iran ta ci gaba da kokarin nuna juriya da maida martani da makamai masu linzami
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Kasar Yahudawa 'yan kama wuri zauna watau Isra'ila ta bayyana cewa yaƙin da take yi da Iran ya shiga “muhimmin mataki na ƙarshe."
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da fashe-fashe da hare-haren makamai masu linzami suka girgiza birane a sassa daban-daban na Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Iran ta shirya yiwa Amurka da Isra'ila abin da ba za su taba mantawa ba

Source: Getty Images
Rahoton Tashar Al-Jazeera ya nuna cewa Ministan tsaron Isra’ila Israel Katz, ya ce yakin da suke da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya shiga muhimmmin mataki.
Iran ta ci gaba da maida martani
Wannan kalamai na zuwa ne yayin da aka kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke Baghdad, babban birnin Iraq, inda aka ga hayaki mai kauri yana tashi daga harabar ofishin.
Rahotanni sun ce wannan shi ne hari na biyu da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka tun bayan fara yaƙin a ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare kan Iran.
Wane mataki aka shiga a yakin Iran?
Da yake jawabi kan halin da ake ciki, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ya ce yaƙin da ake yi da Tehran ya shiga wani muhimmin mataki.
Ya yabawa hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyar fitar da man fetur ta Iran da ke tsibirin Kharg, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu
A cewarsa:
“Yaƙin da ake yi da Iran, karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, yanzu yana kara tsananta kuma ya shiga muhimmin mataki.”
Ya kara da cewa kasashen Amurka da Isra'ila za su ci gaba da kai hare-haren kan Iran muddin akwai bukatar hakan.

Source: Getty Images
Matakan da kasar Iran ta fara dauka
Duk da irin ƙarfin sojin Amurka da Isra’ila, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna cewa ba za ta ja da baya ba.
Rahotanni sun ce Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan ƙasashe akalla 10 a yankin, tare da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar mai muhimmanci ta Strait of Hormuz.
Wannan mashigar ce kimanin kashi 20% na man fetur na duniya ke wucewa ta cikinta, lamarin da ya jefa kasuwannin duniya cikin tashin hankali.
Amurka da Isra'ila sun sake yiwa Iran barna
A wani rahoton, kun ji cewa Amurka da Isra'ila sun hallaka mutane dama da 100 a wasu hare-hare da suka kai lardin Kurdistan a Iran.
Hukumomin kasar Iran sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 112 a hare-haren da Amurka da Isra'i'a suka kai lardin Kurdistan a yayin da musayar wuta ke kara zafi.
Shugaban sashen agajin gaggawa na lardin ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hare-haren jiragen sama da makamai masu linzami.
Asali: Legit.ng
