Harin Tsibirin Kharg: Shugaban Amurka Ya Ga Abin da Bai Yi Tsammani ba a Yaki da Iran
- Masana sun fara bayyana cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi mamakin yadda yakinsa da Iran ke neman kubucewa daga ikonsa
- Wani masani a fannin siyasa daga jami’ar Chicago, Robert Pape ya ce harin da Amurka ta kai tsibirin Kharg ya nuna Trump ya fara rasa iko da yakin
- Ya yi gargadin cewa taba wannan tsibiri na man feturin Iran zai iya jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Masana a kasar Amurka sun fara sharhi kan harin da Shugaba Donald Trump ya ba da umarni aka kai kan tsibirin Kharg da ke Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wani masani a fannin siyasa daga jami’ar Chicago, Robert Pape, ya bayyana cewa Trump ya bada umarnin kai hari kan tsibirin mai na Kharg ne saboda yana kokarin dawo da iko kan yakin da yake ganin yana kubuce masa.

Source: Getty Images
Dalilin Donald Trump na kai hari tsibirin Kharg
A wata hira da ya yi da tashar Al Jazeera, Pape ya ce yana ganin matakin na Trump na iya kasancewa daga cikin kokarin neman wata sabuwar dabara bayan rashin cimma burin farko na yakin.
A cewar Pape, Shugaba Trump ya fara yakin da tsammanin hare-haren za su dauki ‘yan kwanaki kaɗan ne kawai kuma a tunaninsa gwamnatin Iran za ta rushe cikin sauki amma sai ya ga turjiyar da bai yi tsammani ba.
Sai dai daga baya Shugaban Amurka da kansa ya nuna mamaki cewa gwamnatin Iran ba ta rushe ba duk da hare-haren da ake kai mata.
Trump ya gaza cimma manufarsa kan Iran
Masani Robert Pape ya ce:
"Amurka da Isra’ila sun samu nasarori na soji a wasu hare-hare da suka kai kan Iran amma a batun manufofin da suka kudiri aniyar cimmawa yakin, za mu iya cewa sun yi rashin nasara a halin yanzu."
A cewarsa, hakan ne ya sa Trump ke neman sababbin matakai na soji domin cimma nasara kan Iran sabida ya riga ya fadi a lissafin da ya yi tun farko.
Hadarin mamaye tsibirin Kharg na Iran
Pape ya kuma yi gargadi cewa idan Amurka ta yi kokarin tura sojojin ruwa domin kwace tsibirin Kharg, hakan na iya zama babban hadari.
Ya ce:
"Sojojin Amurka za su iya fuskantar ruwan wuta na makamai daga Iran na tsawon lokaci, wanda hakan zai iya kara jawo karuwar asarar rayuka."

Source: Getty Images
Masanin ya kuma yi gargadin cewa kai hare-hare kan tsibirin Kharg, wanda shi ne babban cibiyar fitar da man fetur na Iran, na iya haifar da matsala mai girma ga tattalin arzikin duniya.
"Idan wannan tsibiri ya daina aiki, yawan man fetur a kasuwa zai ragu sosa kuma farashin mai zai tashi a duniya," in ji shi.
Pape ya ce idan hakan ta faru, yakin ba zai zama nasara ga Amurka ba, illa ma zai kara tsananta matsalolin tattalin arziki a duniya, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.
An kara kashe fiye da mutum 100 a Iran
A baya, kun ji cewa hukumomin kasar Iran sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 112 a hare-haren da Amurka da Isra'i'a suka kai lardin Kurdistan.
Shugaban sashen agajin gaggawa na lardin ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hare-haren jiragen sama da makamai masu linzami.
Haka zalika ma’aikatar al’adu ta Iran ta bayyana cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun lalata akalla wuraren tarihi da al’adu 56 a sassan kasar.
Asali: Legit.ng


