Wuta Ta Yi Wuta; Hezbollah Ta Zafafa Hare Hare kan Isra'ila, Ta Bayyana Wuraren da Ta Farmaka

Wuta Ta Yi Wuta; Hezbollah Ta Zafafa Hare Hare kan Isra'ila, Ta Bayyana Wuraren da Ta Farmaka

  • Kungiyar Hezbollah da ke kasar Lebanon na ci gaba da kai hare-hare kan wurare da dama na Isra'ila a ci gaba da yakin da ake yi
  • Hezbollah ta kai wasu hare-hare ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan sansonon sojojon Isra'ila
  • Kungiyar ta bayyana cewa ta kai hare-haren ne a matsayin martani kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa a kasar Lebanon

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Beirut, Lebanon - Kungiyar Hezbollah ta bayyana cewa ta kaddamar da hare-hare 25 na makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa waɗanda suka nufi sansanonin sojojin Isra'ila.

Hare-haren sun kuma nufi matsugunai, wuraren taron dakarun soji a Arewaci da Tsakiyar Isra'ila, da kuma wasu sansanoni kusa da iyakar Kudancin Lebanon.

Hezbollah ta kai hare-hare kan Isra'ila
Mayakan kungiyar Hezbollah da ke Lebanon Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Tashar Anadolu Ajansi ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daban-daban da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Ana azumin Ramadan, Isra'ila ta kashe babban malamin addinin Musulunci

Hezbollah ta kai hare-hare kan Isra'ila

Kungiyar ta ce an kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa a kan birane da ƙauyukan Lebanon da dama, ciki har da unguwannin Kudancin Beirut.

Hezbollah ta ce ta harba makamai maau linzami da jirage marasa matuƙa da dama a garin Nahariya na Isra'ila a lokuta daban-daban na ranar, sannan ta kai hari a Kiryat Shmona ta hanyar harba makamai masu linzami.

Ƙungiyar ta ce ta farmaki barikin Yaara da jirage marasa matuƙa masu kunar bakin wake, sannan ta nufi sansanin kula da sararin samaniya da sa ido na Meron da ke arewacin Isra'ila da jirage marasa matuƙa.

Ta yi ikirarin yi wa Isra'ila barna

Hezbollah ta yi iƙirarin cewa harin ya lalata ɗaya daga cikin na'urorin sanya ido da ba da kariya na sansanin, jaridar The Times of India ta kawo labarin.

Kungiyar ta kuma ce ta kai hare-haren makamani masu linzami kan tsarin kariya na sararin samaniya na Isra'ila a Maalot-Tarshiha, sannan ta nufi matsugunan Admit, Zar’it, Shlomi, da Even Menachem gami da sansanin sojoji na Malkia.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi wa Iran babbar illa: An hallaka babban kwamanda a rundunar IRGC

Hare-haren sun shafi sansanonin sojoji

A tsakiyar Isra'ila, ƙungiyar ta ce ta nufi sansanin sojoji na Beit Lid, wanda ke ɗauke da sansanonin horarwa na dakarun Nahal da na masu laima da makamai masu linzami.

Hezbollah ta farmaki sansanonin sojojin Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Haka kuma ta ce ta farmaki sansanin Glilot, wanda ke ɗauke da hedkwatar rundunar leƙen asirin sojin Isra'ila ta Unit 8200 kusa da Tel Aviv, da kuma tsarin kariya na sararin samaniya kusa da birnin Caesarea.

A Kudancin Lebanon, Hezbollah ta ce ta farmaki taron dakarun sojojin Isra'ila a wurare da dama kusa da iyaka, ciki har da Merkaba, Blat, Tel al-Hamamess, Jabal Warda, da Adaisseh ta hanyar amfani da makamai masu linzami da manyan bindigogi.

Isra'ila ta kashe kwamandan IRGC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Isra'ila sun kashe wani kwamandan gudanarwa a rundunar IRGC ta Iran.

Abu Dharr Mohammadi ya kasance kwamandan sashin makamai masu linzami na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran dake aiki a cikin ƙungiyar Hezbollah.

An bayyana shi a matsayin mutum mai muhimmanci wajen gina dabarun yaƙi da ƙarfafa makaman linzamin Hezbollah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng