Iran Ta Harzuka, Ta Bayyana Sababbin Wuraren da Za Ta Farmaka a Isra'ila
- Yakin da ake gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya bai nuna alamun cewa za a kawo karshensa a nan kusa
- Kwamanda a rundunar IRGC ta kasar Iran, Janar Majid Mousavi, ya lissafo sababbin wuraren da za su kai wa hari a Isra'ila
- Janar Majid Mousavi ya bayyana cewa a duk lokacin da makiyi ya yi kuskure, ba za su yi wata-wata ba wajen zakulo sababbin wuraren da za su farmaka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Kwamandan dakarun sararin samaniya na rundunar kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), Janar Majid Mousavi, ya bayyana sababbin wuraren da za su farmaka a kasar Isra'ila.
Janar Majid Mousavi ya sanar da cewa wuraren hako iskar gas na Isra'ila da ke Leviathan da Karish, waɗanda ke cikin tekun Mediterranean, sun zama wuraren da za a kai wa hari.

Source: Getty Images
Janar Majid Mousavi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.
Iran za ta farmaki sababbin wurare a Isra'ila
Ya bayyana cewa wuraren hako iskar gas din sun zamu sababbin wuraren da za su fuskanci hari daga rundunar IRGC.
Janar Majid Mousavi ya nuna cewa ba a iya wadannan wuraren za su tsaya ba, akwai wasu wurare da dama da za su farmaka.
Kwamandan na IRGC ya bayyana waɗannan wuraren guda biyu na hako iskar gas, tare da wasu sababbin wurare da dama suna cikin jerin abubuwan da za su kai wa hari.
“A duk lokacin da maƙiyi ya ƙara yin kuskure, za a buɗe wasu sabbin fagagen yaƙi a kansa."
- Janar Majid Mousavi
Iran ta yi gargadi mai zafi
Tun da farko, tashar Aljazeera ta cemai magana da yawun babban hedkwatar rundunar sojojin Iran ta Khatam al-Anbiya, Ebrahim Zolfaqari, ya yi gargadin kada a kuskura a farmaki kayayyakin samar makamashi na Iran.

Kara karanta wannan
Ganin fetur ya tashi a duniya, Tinubu ya bada umarnin gaggawa a kawo wa 'yan Najeriya sa'ida
Ya bayyana cewa za su sanya wa wuraren man fetur da iskar gas na yankin Gabas ta Tsakiya wuta idan har aka kai ko da “ƙaramin” hari ne kan kayayyakin samar makamashi ko tashoshin jiragen ruwan Iran.
“Muna gargaɗin gwamnatin da ta ke ka hari da dukkan kawayenta cewa, ƙaramin hari kan kayayyakin samar da makamashi da tashoshin jiragen ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai fuskanci martani mai girma daga gare mu."
- Ebrahim Zolfaqari

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa idan har aka kai irin wannan harin, “dukkan kayayyakin more rayuwa na mai da iskar gas na yankin,” waɗanda Amurka da ƙawayenta na Yamma suke da hannu jari a cikinsu, za a “sanya musu wuta tare da lalata su.”
Mojtaba ya aika sako ga kasashen Larabawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya aika da sakon gargadi ga kasashen Larabawa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Mojtaba Khamenei ya bukaci a gaggauta rufe dukkanin sansanonin sojojin Amurka da ke a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sabon jagoran addinin na Iran, ya yi gargaɗin cewa idan ba rufe sansanonin ba, za su zama wuraren da Iran za ta ci gaba da kai wa hari.
Asali: Legit.ng
