Babbar Magana: Babban Jirgin Daukar Jiragen Yakin Amurka Ya Kama da Wuta, an Samu Bayanai
- Jirgin ruwan daukar jiragen yakin Amurka, USS Gerald R. Ford, ya gamu da gobara a cikin teku a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026
- Babban jirgin yana taimakawa a 'Operation Epic Fury' wanda Amurka da Isra'ila suka kaddamar ta hanyar kai hare-hare kan kasar Iran
- Hukumomi sun yi bayani kan ko tashin gobarar na da alaka da yakin da ake fafatawa, yayin da suka ce wasu sojoji sun jikkata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Wata gobara ta tashi a cikin jirgin ruwan ɗaukar jiragen yaƙi na USS Gerald R. Ford (CVN-78).
Gobarar ta tashi a cikin babban jirgin ruwan daukar jiragen yakin a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.

Source: Getty Images
Rundunar sojojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, US Central Command ta bayyana hakan a shafinta na X.
Meyasa jirgin Amurka ya kama da wuta?
An riga an kashe gobarar ta farko, amma ma'aikatan jirgin suna ci gaba da ƙoƙarin shawo kan ɓarnar da aka yi.
Sanarwar na cewa:
“A ranar 12 ga Maris, USS Gerald R. Ford (CVN 78) ya fuskanci gobara wadda ta samo asali daga sashen wanki na babban jirgin."
“Dalilin tashin gobarar ba shi da alaƙa da fafatawar yaƙi kuma an shawo kanta. Babu wata ɓarna da ta samu injinan jirgin, kuma jirgin ɗaukar jiragen yaƙin yana nan yana gudanar da ayyukansa gaba ɗaya."
"Sojojin ruwa guda biyu ne a halin yanzu suke karɓar magani sakamakon raunukan da ba su kai ga barazanar rayuwa ba, kuma suna cikin yanayi mai kyau. Za a bayar da ƙarin bayani idan aka samu.”
Jirgin na taimakawa a yakin Iran
Tashar USNI News ta ce ya zuwa ranar Laraba, jirgin na Ford yana gudanar da ayyuka ne a yankin Arewacin tekun Red Sea, kusa da gabar tekun Al Wajh na ƙasar Saudiyya, kamar yadda wani mai lura da zirga-zirgar jiragen ruwa ya bayyana.
Jirgin na Ford wanda yake tare da wasu jiragen yaƙi guda uku masu rakiya, USS Mahan (DDG-72), USS Bainbridge (DDG-96) da kuma USS Winston S. Churchill (DDG-81), sun ratsa ta mashigar ruwa ta Suez Canal a makon da ya gabata.
Jirgin ruwan na Ford tare da tawagarsa na taimakawa a aikin soja na "Operation Epic Fury", wato yaƙin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran wanda ke gab da kammala makonsa na biyu.
USS Gerald Ford ya dade a Gabas ta Tsakiya
An tura jirgin tun watan Yunin 2025 kuma an tsawaita zaman sa sau da dama.

Source: Getty Images
A watan da ya gabata, ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta tsawaita zaman na Ford tare da ba shi aikin komawa Gabas ta Tsakiya kafin fara yaƙi da Iran.
Idan har jirgin na Ford ya ci gaba da zama har zuwa tsakiyar watan Afrilu, zai karya tarihin kwanaki 294 na zaman jirgin ɗaukar jiragen yaƙi a aiki tun bayan yaƙin Vietnam.
Jirgin USS Abraham Lincoln (CVN-72) ne ya kafa wannan tarihin a shekarar 2020.
Idan har jirgin ya zauna har zuwa farkon watan Mayu, zai yi gogayya da zaman kwanaki 300 da jiragen ɗaukar jiragen yaƙi suka yi a lokacin yaƙin Vietnam a yankin Gulf of Tonkin.

Kara karanta wannan
Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko
Iran na son a rufe sansanonin sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya aika da sakon gargadi ga kasashen Gabas ta Tsakiya.
Mojtaba Khamenei ya bukaci kasashen da su rufe sansanonin sojojin Amurka ko kjma su ci gaba da farmakarsu.
Ya bayyana cewa hare-haren da Iran ke kai wa, tana kai su ne kan sansanonin sojojin Amurka ba wai ga kasashen ba.
Asali: Legit.ng

