Kasashen da Ke Goyon Bayan Iran a Yakin da Ta Ke Yi da Amurka da Isra'ila
Birnin Tehran, Iran - A ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026, kasashen Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare ta sama a kan Iran.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
An kashe wa Iran Ayatollah Khamenei
Tashar NBC News ta ce a farkon ranar Lahadi, 1 ga watan 2026, Iran ta sanar da mutuwar Khamenei, mai shekaru 86, biyo bayan harin bam da Amurka da Isra'ila suka kai wa birnin Tehran.
Haka kuma ta ayyana kwanaki 40 na zaman makoki a ƙasar.
Majalisar koli ta tsaro ta Iran ta ce an kashe Khamenei ne a ofishinsa da safiyar ranar Asabar, kuma mutuwarsa za ta zama mafarin wani “babban tawaye ga azzaluman duniya.”

Kara karanta wannan
Yaki da canza salo, Iran ta sauya dabarun kai hare hare kan sansanonin Amurka da Isra'ila
Kasashen da suka nuna goyon baya ga Iran
Bayan barkewar yakin, an samu kasashen da suka fito suka yi Allah wadai da hare-haren tare da nuna goyon bayansu ga Iran.
Kasashen sun nuna cewa yakin ya sabawa dokokin kasa da kasa na duniya, kuma bai kamata a farmaki Iran ba.
Mafi yawan kasashen dai abokan huldar Iran ne, inda suke da dangantaka mai karfi a tsakaninsu.
Ga jerinsu nan kasa:
1. Rasha
Rasha ta samu matsayin babbar abokiyar ciniki kuma mai samar da makamai da fasaha ga Iran, wadda ta fuskanci takunkumin ƙasa da ƙasa mai tsanani.

Source: Getty Images
Rasha ta yi Allah-wadai da hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran a matsayin wani mataki na cin zarafi da makamai wanda aka tsara tun da fari kuma ba tare da wani dalili ba ga wata ƙasa mai cin gashin kanta kuma mamba a majalisar dinkin duniya.
Tashar AP News ta ce a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar, ta zargi Washington da Tel Aviv da "ɓuya a bayan" damuwa game da shirin nukiliyar Iran yayin da a zahiri suke neman kifar da gwamnati.

Kara karanta wannan
Iran ta harba makamai masu linzami kan babban birnin Isra'ila, an ji barnar da suka yi
Ta bukaci a dakatar da yakin cikin gaggawa tare da komawa kan teburin tattaunawa ta diflomasiyya.
2. China
China ta yi Allah-wadai da kisan Jagoran addini na Iran Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila suka kai kan babban birnin Iran.

Source: Getty Images
Ma'aikatar harkokin wajen kasar China a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa hare-haren da kisan Ayatollah Ali Khamenei, tauye hakkin ikon kasar Iran ne, tashar Anadolu Ajansi ta kawo labarin.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Harin da kisan jagoran addini na Iran babban tauye hakkin ikon ƙasar Iran ne da tsaron ta.
“Hakan ya take manufofi da ƙa’idojin yarjejeniyar majalisar dinkin duniya da ƙa’idojin dangantakar ƙasa da ƙasa. China tana adawa da hakan kuma tana tir da harin."
3. Pakistan
Mataimakin Firaministan Pakistan kuma Ministan harkokin waje, Ishaq Dar, ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “hare-haren da ba su da dalili” kan Iran da Isra’ila da Amurka suka kai, inda ya bukaci a dakatar da rikicin cikin gaggawa.

Source: Getty Images
Ministan harkokin wajen ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin Mofa.gov.pk
Ishaq Dar ya yi Allah-wadai da kakkausan harshe kan hare-haren da ba su da dalili kan Iran kuma ya yi kiran da a dakatar da ƙaruwar rigingimu ta hanyar komawa tattaunawar diflomasiyya cikin gaggawa domin cimma matsaya ta zaman lafiya.
Pakistan ta bayyana cewa Iran tana da haƙƙin kare kanta a ƙarƙashin yarjejeniyar majalisar dinkin duniya, yayin da take kira ga dukkan ɓangarorin da su hakura da yaki.
4. Turkiyya
Shugaban Turkiyya, Tayyip Erdogan a ranar Litinin ya soki hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran a matsayin katsalandan ga dokokin ƙasa da ƙasa.

Source: Getty Images
Erdogan ya kara da cewa Turkiyya tana jimamin raɗaɗin da al’ummar Iran ke ciki a daidai lokacin da yaƙin ke faɗaɗa, tashar Reuters ta kawo labarin.
A cikin mafi ƙarfin adawarsa ga yakin, Erdogan ya ce hare-haren sun keta dokokin ƙasa da ƙasa.
“A matsayinmu na maƙwabta kuma 'yan’uwa, muna taya al’ummar Iran jimamin raɗaɗin su."
- Tayyip Erdogan
5. Koriya ta Arewa
Koriya ta Arewa ta yi Allah-wadai da hare-haren Amurka da Isra'ila a matsayin wani haramtaccen mataki na cin zarafi.

Source: Getty Images
Kakakin ma'aikatar wajen Koriya a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa hare-haren sun zama cikakken haramtaccen mataki na cin zarafi kuma mafi munin nau'i na keta ikon ƙasa, shafin News.am ya kawo labarin.
Koriya ta Areawa ta zargi Amurka da Isra'ila da nuna halin rashin kunya da na ’yan daba da kuma yin amfani da ƙarfin soja wajen cika "burinsu na son kai da mulkin mallaka".
Iran ta kafa sharuddan daina yaki da Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya kafa sharuddan kawo kawo karshen yakin kasarsa da Amurka da Isra'ila.
Masoud Pezeshkian ya lissafa sharuɗɗa guda uku da ƙasarsa ke buƙata domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi yanzu da Amurka da Isra’ila.
Shugaban na Iran ya ambaci ɗaya daga cikin sharuɗɗan a matsayin “biyan diyyar asara” da Amurka za ta yi na barnar da ta haddasa wa Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

