Tuna Baya: Yadda Isra'ila Ta kai Hari kan Jirgin Amurka Ta Kashe Sojoji

Tuna Baya: Yadda Isra'ila Ta kai Hari kan Jirgin Amurka Ta Kashe Sojoji

  • A watan Yuni na shekarar 1967, wani jirgin ruwan rundunar sojin ruwan Amurka ya fuskanci hari daga sojojin Isra’ila a tekun kasa da kasa kusa da yankin Sinai
  • Harin ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka da farar hula 34, yayin da wasu 171 suka jikkata, lamarin da ya zama daya daga cikin mafi munin abubuwan ga sojin ruwan Amurka
  • Shekaru da dama bayan harin, har yanzu lamarin na jawo ce-ce-ku-ce, inda ake ci gaba da nuna shakku kan ko harin kuskure ne ko kuma da gangan aka kai shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - A ranar 8 ga Yuni, 1967 sojojin Isra’ila suka kai wani mummunan hari kan wani jirgin ruwan leken asiri na rundunar sojin Amurka.

An kai harin ne a ruwan kasa da kasa kusa da yankin Sinai, inda aka kashe sojoji da masu nazarin bayanai na Amurka 34, sannan wasu 171 suka jikkata.

Kara karanta wannan

Yadda bama baman Iran suka jikkata sojojin Amurka 150 a fagen yaki

Jirgin Amurka da Isra'ila ta kaiwa hari
Jirgin Amurka da Isra'ila ta kaiwa hari a shekarar 1967. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kundin Britannica ya bayyana cewa jirgin USS Liberty yana da alamomin da ke nuna shi na Amurka ne a fili, yana dauke da tutar kasar kuma yana dauke da lambar jikinsa GTR-5 a gaba da baya.

Duk da haka, jiragen yaki da kwale-kwalen harba makamai na Isra’ila sun kai masa hari da manyan bindigogi, lamarin da ya sa jirgin kamawa da wuta.

Jirgin Amurka da Isra'ila ta farmaka

Bincike ya nuna cewa Jirgin USS Liberty na kasar Amurka da aka fito da shi a karshe-karshen yakin duniya na biyu ya fara aiki da suna SS Simmons Victory.

Bayan yakin, an cire manyan bindigoginsa, sannan ya ci gaba da aiki a matsayin jirgin dakon kaya na farar hula har zuwa shekarar 1958. A shekarar 1963, rundunar sojin ruwa ta Amurka ta karbe shi tare da sake masa suna USS Liberty.

A karshen watan Mayu na shekarar 1967, Hukumar Tsaron Kasa ta Amurka (NSA) ta tura jirgin zuwa gabashin Tekun Bahar Rum domin sa ido kan sakonnin rediyo na kasashen Larabawa yayin da tashin hankali ke karuwa tsakanin su da Isra’ila.

Kara karanta wannan

An harba rokoki kan dakarun Isra'ila, sojojin Netanyahu sun mutu

Jirgin yana dauke da na’urori masu yawa, kuma aikinsa shi ne tattara bayanan sirri kawai. Kuma a lokacin ba a ba shi aikin sa ido kan sakonnin Isra’ila ba.

Benjamin Netanyahu da Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump da Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A daidai lokacin ne yakin da aka yi na kwana shida ya barke a ranar 5 ga Yuni, 1967 a lokacin da Isra’ila ta kai hare-haren sama na farko kan Masar, Siriya da Jordan.

Isra'ila ta kai hari kan Amurka

A ranar 8 ga Yuni, jirgin Liberty yana tafiya a ruwan kasa da kasa kusa da yankin Sinai. Jiragen leken asirin Isra’ila suka fito suna shawagi a samansa, yayin da tutar Amurka da lambar jirgin GTR-5 suke bayyane a fili.

Da karfe 3:05 na rana, jiragen yakin Isra’ila suka bude wuta kan jirgin da manyan bindigogi, inda suka lalata kananan makaman kariya da na’urorin sadarwarsa.

Da karfe 3:20 na rana, wasu kwale-kwalen yaki uku na Isra’ila masu harba makamai suka shiga harin, inda suka harba makamai masu linzami kan jirgin.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya ci gaba har zuwa karfe 4:30 na yamma, lokacin da Isra’ila ta ce ta gano cewa jirgin na Amurka ne.

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Amurka gagarumar barna, Trump zai je karbar wadanda aka kashe

Tashar Al-Jazeera ta wallafa cewa gaba daya, ma’aikatan jirgin da masu nazari da tattara bayanai 34 sun mutu, yayin da wasu 171 suka jikkata.

Sojojin Iran sun ja kunnen Amurka

Shekaru bayan 50 da wancan labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Iran sun gargadi Shugaban Amurka, Donald Trump game da batun tsayar da yakin da suka fara.

Amurka ta bayyana cewa yakin ya kusa zuwa karshe, inda Donald Trump ya ce sun gama cin nasara a kan Iran a kasa da mako biyu.

A kan haka ne Iran ta ce maganar tsayar da yakin yana hannunta, kuma babu wanda zai iya tabbatar da magannar tsagaita wuta sai ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng