Makaman Iran Sun Dura kan Tankar Man Amurka a Teku, Ta Kama da Wuta
- Yakin Amurka/Isra'ila da Iran na cigaba da daukan sabon salo bayan shiga rana ta shida ana fafatawa tsakanin juna da kai hare-hare
- Amurka ta sanar da nutsar da wani jirgin ruwan Iran da ya dauko hanya daga Indiya zai dawo gida bayan gayyata da aka masa zuwa kasar
- Da safiyar yau Alhamis, 5 ga watan Maris rundunar juyin juya hali ta Iran ta sanar da ramuwar gayya kan wani jirgin ruwa dauke da man Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Sa’o’i kadan bayan kai hari kan wani jirgin ruwan yaki na Iran a Tekun Indiya, rundunar IRGC ta Iran ta sanar da cewa ta yi ramakon gayya.
Hakan na zuwa ne bayan shafe kwana shida suna fuskantar juna da hare-hare, lamarin da ya shafi kasashen Gabas ta Tsakiya da dama.

Source: Getty Images
Rahoton India Today ya nuna cewa tun da farko kasar Iran ta sanar da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar fansar abin da aka mata a Tekun India.
Iran ta farmaki tankar man Amurka
Reuters ta rahoto cewa dakarun Iran sun sanar da cewa sun kai hari kan wani jirgi dauke da tankar man Amurka a Arewacin Tekun Farisa.
Kafofin yada labaran gwamnatin Iran sun ce jirgin Amurkan ya kama da wuta bayan dirar mikiya da suka masa a shirin daukar fansa.
Harin ya zo ne bayan ministan harkokin wajen Iran ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi nadama kan harin da aka kai kan jirgin ruwansu mai suna IRIS Dena a gabar tekun Sri Lanka.
Amurka ta kai hari kan jirgin Iran ne bayan rundunar IRGC ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ta dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz.
Wannan lamari na nuna karuwar tashin hankali a rikicin da zuwa yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Iran, tare da mutuwar wasu sojojin Amurka.
Yadda Amurka ta nutsar da jirgin Iran
Jirgin ruwan yakin Iran mai mai suna RIS Dena na kan hanyarsa ta komawa Tehran daga birnin Visakhapatnam na kasar Indiya bayan ya halarci atisayen sojojin ruwa guda biyu a watan da ya gabata.
A lokacin ne wani makami mai linzami daga jirgin ruwan Amurka ya same shi. Harin ba-zatan da aka kai a ruwan kasa-da-kasa ya yi sanadin mutuwar matukan jirgin Iran 87.

Source: Getty Images
An samu kwamandan jirgin IRIS Dena tare da wasu manyan jami’ai daga cikin mutane 32 da da suka tsira, yayin da sama da ba a ga mutane 60 ba har yanzu.
Iran: Amurka ta rufe ofis a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da aiki da rufe ofishinta da ke babban birnin Najeriya Abuja.
Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke cigaba da kai farmaki kan kadarorin Amurka a kasashe daban-daban kan kashe Ayatollah Khamenei.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya ce ya dakatar da aiki ne saboda fargabar barkewar zanga-zangar goyon bayan Iran a Abuja.
Asali: Legit.ng

