Baya Ta Haihu: Amurka Ta Zare Hannu a Kashe Khamenei, Ta Fadi Mai Laifi
- Ma'aikatar yakin Amurka ta yi karin bayani game da kashe jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei yayin da ake cigaba da yaki
- Ta bayyana cewa ba harin ta ba ne ya kashe shi duk da ikirarin da Shugaba Donald Trump ya yi na cewa su suka kai harin da ya jawo rasa rayuwarsa
- Amurka ta fadi wadanda ta ce su suka kashe shi a daidai lokacin da sojojin Iran ke cigaba da harba makamai sansaninta da ke Gabas ta Tsakiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Ma’aikatar Yakin Amurka (Pentagon) ta nesanta kanta daga kashe Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Hassan Khamenei.
An kai hari hari kasar Iran a ranar Asabar da ta wuce, inda Shugaba Donald Trump ya fito karara ya ce su ne suka kai farmaki suka kashe Khamenei.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance

Source: Getty Images
RFI ta rahoto cewa duk da ikirarin da Trump ya yi, babban jami'in Amurka, Elbridge Colby ya fito ya ce ba da hannunsu aka kashe Ayatollah Ali Khamenei ba.
Wa ya kashe Ali Khamenei a Iran?
Yayin da yake bayar da shaida a gaban kwamitin sojoji na majalisar dattawan Amurka a ranar Talata, babban jami’in tsara manufofi a Pentagon, Elbridge Colby, ya ce harin da ya kashe Khamenei ba ya cikin tsarin Amurka.
“Waɗannan ayyuka ne na Isra’ila,”
National Post ta ruwaito Colby na mayar da martani ga ‘yan majalisa da suka matsa masa kan ko sauya tsarin mulki a Iran na daga cikin manufofin Amurka.
Trump ya ce sun kashe Khamenei
Salon jawabin Colboy ya bambanta da na Shugaba Donald Trump, wanda tun bayan fara hare-haren yake bayyana rikicin da kalamai masu zafi da nuna nasara.
“A tsawon shekaru 47, gwamnatin Iran tana fatan rushewa ga Amurka tare da gudanar da yaƙin zubar da jini da kisan gilla ba kakkautawa,”
- Inji Trump a ranar Asabar.
A wani saƙo da ya wallafa bayan mutuwar Khamenei, Trump ya ce:
“Khamenei ya kasa tserewa daga tsarin leƙen asirinmu da kuma hanyoyin sa ido na zamani,”
Ya ƙara da cewa:
“Tare da aiki kafada da kafada da Isra’ila, babu abin da shi ko sauran shugabannin da aka kashe tare da shi za su iya yi.”

Source: Facebook
Abin da ministan Amurka ya ce
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ma ya ce sun shiga lamarin ne bayan samun labarin cewa Isra’ila na shirin kai hari, abin da ke nuna Amurka ta taka rawa.
Ya bayyana cewa manyan wuraren da ake kai hari sun haɗa da makaman roka na Iran — waɗanda ya ce sun ƙaru sosai — da kuma ƙarfin ƙasar na kera waɗannan makamai, tare da wasu sassan rundunar ruwan Iran.
Amurkawa sun makale a Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta bayyana karara cewa ba za ta iya ceto 'yan kasarta da ke kokarin gudu daga Isra'ila ba.
Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke cigaba da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka bayan hari da aka kai mata.
Amurka ta ce gwamnatin Isra'ila ta samar da motocin da za a iya shiga domin barin kasar, amma ba za ta jagoranci wani ya shiga motocin ba.
Asali: Legit.ng

