Yaki Ya Rincabe a Rana Ta 4, Iran Ta Farmaki Amurkawa a Saudiyya
- An shiga rana ta hudu a cigaba da gwabza yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran, inda aka kai hari ofishin Jakadancin Amurka a kasar Saudiyya
- Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta fitar da sanarwa game da 'yan kasarta da ke zaune a kasar Saudiyya bayan harin da Iran ta kai ofishinta
- Shugaba Donald Trump ya nuna damuwa game da harin, inda ya bayyana cewa nan gaba kadan duniya za ta ga martanin da Amurka za ta yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Hare-haren da Iran ke kaiwa kasashen Gabas ta Tsakiya na cigaba da shafar biranen Saudiyya da Amurka ke da kadarori.
An samu rahoton cewa an harba makamai a birnin Riyadh kuma ya yi nasarar lalata kadarorin Amurka, lamarin da ya tilasawa kasar fitar da sanarwa.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta rahoto cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai yi martani game da abin da ya faru kuma duniya za ta gani a kasa.
An farmaki ofishin Amurka a Saudi
Rahotanni sun ce an ji ƙarar abubuwan fashewa biyu a Riyadh, bayan hukumomin Saudiyya sun tabbatar da kai hari kan ofishin jakadancin Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito hakan, inda ya ambaci wasu majiyoyi masu inganci da suka tabbatar masa da lamarin.
Kira ga Amurkawa a Saudiyya
Hukumomin Amurka sun buƙaci ‘yan ƙasarsu da ke wasu biranen Saudiyya da su zauna a inda suke, tare da guje wa zuwa ofishin jakadancin da ke Riyadh, bayan jirage marasa matuƙa guda biyu sun kai hari kan wurin.
A wani saƙo da ofishin jakadancin ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce:
“Ofishin Amurka a Saudiyya ya fitar da sanarwar kowa ya zauna a inda yake ga biranen Jeddah, Riyadh da Dhahran, tare da takaita tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa duk wasu sansanonin soji a yankin.

Kara karanta wannan
Trump ya fadi adadin shugabannin Iran da aka kashe, ya bayyana mamakin da kasar ta ba shi
"Muna ba ‘yan Amurka da ke kasar shawarar su zauna a inda suke nan take, kuma su guji ofishin jakadanci har sai an bayar da wata sanarwa, sakamakon harin da aka kai kan wurin.”
Yayin tabbatar da hai kan ofishin jakadancin Amurka, hukumomin Saudiyya sun ce harin ya haddasa “ƙaramar gobara” da kuma lalacewa kaɗan.
Trump: 'Martanin Amurka na tafe'
‘Yar jarida Kellie Meyer ta ce Donald Trump ya shaida mata cewa za su dauki mataki bayan harin da aka kai musu a kasar Saudiyya nan gaba kadan.

Source: Getty Images
Meyer ta ƙara da cewa Trump ya ce bai yi tunanin tura sojojin ƙasa zai zama dole ba a yaƙin da ake yi da Iran, duk da cewa tun da farko ya bayyana cewa bai yi nazarin yiwuwar tura sojoji ba.
An farmaki matatar mai a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta kai wasu hare-hare kan matatar mai a kasar Saudiyya yayin da ake cigaba da gwabza yaki da Amurka/Isra'ila.
An dakatar da aiki na wani lokaci a matatar bayan harin, sai dai Saudiyya ta ce ta shawo kan matsalar daga baya kuma ta kashe wutar da ta tashi.
Masana sun yi magana game da harin Iran kan wuraren da ke da alaka da fetur, inda suka ce hakan na iya jawo tashin farashin makamashi a duniya.
Asali: Legit.ng
