Yadda Khumeinei ya Gana da Buhari, Wasu Shugabannin Afrika 9 Kan Muhimman Al'amura

Yadda Khumeinei ya Gana da Buhari, Wasu Shugabannin Afrika 9 Kan Muhimman Al'amura

  • Ayatollah Ali Khamenei ya gana da shugabannin Afirka fiye da goma a lokacin mulkinsa da ya shafe tsawon shekaru
  • Tattaunawa a ganawar tasa da shugabannin ta mayar da hankali ne kan hadin kai da rage dogaro da kasashen yamma irinsu Amurka
  • Daga cikin wadanda ya hadu da su akwai marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Zuma da Mugabe a lokuta daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ayatollah Ali Khamenei, Jagoran addinin Islama na kasar Iran, ya gana da shugabannin kasashen Afirka da dama a tsawon shekaru kafin a kashe shi a wani hari da sojojin Amurka da Isra’ila suka kai a makon nan.

Legit.ng ta rawaito cewa, an tabbatar da rasuwar Khamenei bayan hare-haren Amurka da Isra’ila, lamarin da ya jawo ayyana kwanaki 40 na zaman makoki a Iran.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin ‘yan uwansa, ciki har da diyarsa da jikansa, sun mutu a harin na ranar Asabar 28 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

An 'gano' waɗanda suka taimaka wa Isra'ila da Amurka har aka hallaka Khamenei

Ganawar Khumeinei da shugabannin Afrika
Ganawar Khumeinei da Muhammadu Buhari | Hoto: @VITALIS_77
Source: Twitter

Zanga-zanga a Bagadaza

An samu zanga-zanga a birnin Bagadaza inda masu zanga-zanga suka yi artabu da jami’an tsaro sakamakon tashin hankali bayan mutuwar Khumeinei.

Kafin rasuwarsa, Khamenei ya shafe shekaru yana tattaunawa da shugabannin Afirka kan hadin kai, ra’ayoyin siyasa da kuma hanyoyin rage dogaro da kasashen yamma.

A cewar Africa View Facts, marigayi jagoran Islama na Iran ya gana da shugabannin Afirka sama da 10.

Ganawar Khamenei da shugabannin Afirka

Jerin ganawar da aka rubuta cewa Khamenei ya yi da shugabannin Afirka ya hada da:

  1. Aljeriya – Abdelaziz Bouteflika (2008, 2010)
  2. Afirka ta Kudu – Jacob Zuma (2016)
  3. Benin – Boni Yayi (2012, wanda kuma shi ne shugaban AU a lokacin)
  4. Burundi – Pierre Nkurunziza (2013)
  5. Sudan – Omar al-Bashir (2011)
  6. Zimbabwe – Robert Mugabe (2006)
  7. Najeriya – Muhammadu Buhari (2015)
  8. Ghana – John Dramani Mahama (2016)
  9. Eritrea – Isaias Afwerki (2008)
  10. Djibouti – Ismail Omar Guelleh (2006)

Kara karanta wannan

Khamenei da manyan shugabannin tsaron Iran 4 da suka rasu, ya rasa wasu iyalansa

Amurka da tsoma baki a lamurran kasashen waje

Ba wannan ne karon farko da Amurka ke farmakar kasashen duniya tare da hallaka shugabanninsu ba a tarihi, hakan ya sha faruwa.

A shekarun baya, gwamnatin Amurka a karkashin George W Bush ta zargi shugaban Iran na wancan lokacin, Saddam Husseini da mallakar makamin nukiliya tare da hallaka shi.

Hakazalika, a baya-bayan nan gwamnatin Trump ta shiga har Venezuela tare da dauke shugaban kasar bias zargin ta’ammuli da kayan maye da zalunci a kasar.

Ya zuwa yanzu, shugaban kasa hannun Amurka, inda ake ci gaba da kai ruwa rana kan makomarsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kasashe da dama na nuna Alla-wadai da abin da Amurka ke yi, sai dai kasashen Larabawa da ke zagaye da Iran na ci gaba da zama makusantan Amurka da kut-da-kut.

An nada magajin Khumeinei a Iran

A wani labarin, kun ji cewa an nada Alireza Arafi, daya daga cikin manyan malaman addini kuma mamba a kwamitin Guardian Council, a cikin majalisar rikon shugabancin kasar Iran.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Iran bayan rasuwar jagoran addini, Ayatullah Ali Khamenei

Majalisar rikon shugabancin ita ce ke da alhakin gudanar da ayyukan jagoran kasar har sai Majalisar Kwararru (Assembly of Experts) ta zabi sabon jagora, rahoton Al-Jazeera.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kasar ta sanar rasuwar jagoranta, Ali Khumeinei a wani farmakin Amurka da Isra’ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng