Iran ta Nada Shugaban Riko da Zai Maye Gurbin Jagora Khumeinei na Wucin Gadi

Iran ta Nada Shugaban Riko da Zai Maye Gurbin Jagora Khumeinei na Wucin Gadi

  • An nada Alireza Arafi a cikin majalisar rikon shugabancin Iran bayan rasuwa jagora Ali Khumeinei a farmakin Amurka da Isra’ila
  • Majalisar na rike da mukamin jagoran koli har sai an zabi sabon shugaba kamar yadda tsarin siyasa da shuganancin kasar yake
  • Zai yi aiki tare da Shugaba Pezeshkian da babban alkalin kotun koli Mohseni-Ejei, kamar yadda rahotanni suka bayyana

Tehran, Iran – An nada Alireza Arafi, daya daga cikin manyan malaman addini kuma mamba a kwamitin Guardian Council, a cikin majalisar rikon shugabancin kasar Iran.

Majalisar rikon shugabancin ita ce ke da alhakin gudanar da ayyukan jagoran kasar har sai Majalisar Kwararru (Assembly of Experts) ta zabi sabon jagora, rahoton Al-Jazeera.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kasar ta sanar rasuwar jagoranta, Ali Khumeinei a wani farmakin Amurka da Isra’ila.

Yadda aka maye gurbin Khumeinei na wucin gadi
An nada shugaban rikon kwarya na Iran, Alireza | Hoto: Wikimedia Commons
Source: UGC

Wace rawa Arafi zai taka?

Arafi zai kasance cikin majalisar rikon shugabancin tare da Shugaban kasa, Pezeshkian, da kuma babban alkalin kotun koli, Mohseni-Ejei.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Iran bayan rasuwar jagoran addini, Ayatullah Ali Khamenei

Majalisar na wucin gadi ce, kuma an kafa ta ne domin tabbatar da cewa babu gibin shugabanci a kasar yayin da ake jiran zaben sabon jagoran na kasar.

A halin yanzu, kasar na cikin tashin hankali da jimamin Rashin wannan babban shugaba kuma jagora da ya shafe shekaru wajen gudanar da lamurran kasar.

Farmakin Amurka da Isra’ila kan Iran

A karshen makon nan ne aka samu munanan hare-hare daga Amurka ta hanyar amfani da Isra’ila kan kasar Iran mai cin gashin kanta.

An ruwaito cewa, harin ya kai ga kashe wasu daga cikin manyan shugabanni da masu gudanar da mulkin kasar.

Amurka ta fitar da sanarwar cewa, a halin yanzu ta hallaka Khumeinei ta bakin shugaba Donald Trump, hakazalika bayanai daga sojin Isra’ila.

Iran ta farmaki sansanin Amurka a kasashen Larabawa

A bangare guda, an samu maimaituwar hare-hare ta sama daga Iran zuwa kan sansanin Amurka a kasar Larabawa, ciki har da Saudiyya da Qatar.

Yadda aka maye girbin Khumeinei
Marigayi jagoran Muslunci a Iran, Khumeinei | Hoto: @khumeinei_ir
Source: Twitter

Hakazalika, Iran ta sha alwashin daukar fansar kisa da hare-haren da aka kai mata ba tare da wani laifi ba.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Ya zuwa yanzu, an shiga jimamin kwanaki 40 a kasar, inda tuni dandazon jama’a suka fara rangadin nuna alhini da tofin Alla-tsine ga makasan shugabansu.

Ba wannan ne karon farko da Isra’ila ke kai farmaki kan kasar Iran da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya ba.

An samu irin wannan farmaki kan Iran daga Isra’ila da hadin gwiwar Amurka a shekarar 2025, inda Amurka ta yi ikrarin lalata wurin aikin makamin nukiliya na kasar ta Iran.

Wadanda suka kitsa kashe Khumeinei

A wani rahoto ya bayyana, an gano cewa bayanan sirri na CIA ne suka taimaka wajen jagorantar hare-haren da Amurka da Isra’ila a Iran.

Harin da aka kai ya taimaka wurin hallaka jagoran addinin Musulunci a Iran, Ayatullah Ali Khamenei wanda ya jawo jimami a kasar.

Ba sabon abu bane Amurka ta yi amfani da ‘yan liken asirinta na CIA wajen kai hare-hare a kasashen duniya na tsawon shekaru da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng