Bayan Zargin Faransa, Wadanda Suka kai Hari Nijar Sun Fito Sun Fallasa Kansu

Bayan Zargin Faransa, Wadanda Suka kai Hari Nijar Sun Fito Sun Fallasa Kansu

  • Kungiyar ISIL ta bayyana cewa ita ce ta kai harin bazata a sansanin sojin sama da ke filin jirgin sama na kasa da kasa na Diori Hamani a Niamey
  • Harin ya zo ne a daidai lokacin da Nijar ke fama da hare-haren kungiyoyin ISIL a Sahel da JNIM, lamarin da ke kara tayar da hankali a yankin
  • Masana tsaro sun nuna alamun hadin kai tsakanin mayakan ISIL na Sahel da ISWAP, lamarin da ka iya kara barazanar hare-hare a fadin kasashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nijar – Kungiyar ISIL ta dauki alhakin kai wani hari a sansanin sojin sama da ke babban filin jirgin saman kasar Nijar, kusa da birnin Niamey.

Kungiyar ta bayyana cewa ta kai wani hari na bazata, inda ta yi ikirarin cewa harin ya yi barna mai yawa a sansanin. Sai dai ba a bayar da karin bayani dalla-dalla kan irin barnar da aka yi ko asarar da aka samu ba.

Kara karanta wannan

Tofa: Gwamna ya rufe dukkan makarantu, ya sanya dokar zaman gida ta awanni 20

Abdourahamane Tchiani
Shugaban Nijar, Abdourahamane Tchiani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa maganar daukar alhakin harin ya fito ne ta hannun kafar yada labaran Amaq da ke da alaka da ISIL.

Bayyanar ISIL da halin tsaro a Nijar

Kungiyar ISIL a yankin Sahel ta shahara da kai munanan hare-hare a Nijar a ‘yan watannin baya. Rahotanni sun danganta kungiyar da kashe mutane fiye da 120 a yankin Tillaberi a watan Satumban 2025.

Hukumomin Nijar na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro sakamakon wadannan hare-hare, lamarin da ya janyo kara daukar matakan soja da neman taimakon kasashen waje domin dakile barazanar kungiyoyin masu tayar da kayar baya.

A makon da ya wuce, shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya nuna godiya ga sojojin Rasha da ke sansanin, yana mai cewa sun kare yankin da kyau.

Nazarin masana kan bidiyon ISIL

Masani kan harkokin tsaro, Dr Audu Bulama Bukarti, ya bayyana cewa wani bidiyo da ISIL ta fitar dauke da ikirarin daukar alhakin harin na dauke da murya a harsuna uku, Larabci, Kanuri da Hausa.

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

A cewarsa, harshen Hausa da aka ji a bidiyon na dauke da irin maganar 'yan Najeriya, ba na Nijar ba, yayin da jimlar Kanuri guda daya da aka yi amfani da ita ke da sauti irin na mutanen Borno.

Bukarti ya wallafa a X cewa wannan na nuni da yiwuwar shigar mayakan ISWAP cikin harin, tare da nuna karuwar hadin kai tsakanin ISIL na Sahel da ISWAP.

Audu Bulama Bukarti
Masanin tsaro, Bulama Bukarti na jawabi a taro. Hoto: Audu Bulama Bukarti
Source: Facebook

Masani ya jaddada cewa domin dakile tsananin tsaro, Nijar na bukatar yin aiki kafada da kafada da makwabtanta, ciki har da Najeriya, ta hanyar musayar bayanan sirri, sa ido kan iyakoki da kuma hadin gwiwar yaki da ta’addanci.

Ga bidiyon maganar da 'yan ta'addan suka yi a kasa:

Nijar ta zargi Faransa, kasashe 2

A wani labarin, kun ji cewa Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi Faransa, Benin da Ivory Coast da daukar nauyin harin da aka kai kasarsa.

A cikin wani jawabi a gidan talabijin na gwamnati, ya ce ya kamata wadannan kasashe su kasance a shirye domin fuskantar martanin Nijar.

Duk da maganar da Janar Abdourahamane Tchiani ya yi, babu daya daga cikin kasashen da ya zarga da ta fito da masa martani kan harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng