Uganda Za ta Ci gaba da Hana ‘Yan Kasar awa Kafafen Sada Zumunta Duk da Kammala zabe

Uganda Za ta Ci gaba da Hana ‘Yan Kasar awa Kafafen Sada Zumunta Duk da Kammala zabe

  • Gwamnatin Uganda ta ce za ta ci gaba da takaita amfani da kafafen sada zumunta duk da dawowar intanet bayan zabe
  • An rufe intanet kwanaki biyu kafin bude rumfunan zabe domin dakile yaduwar labaran bogi
  • Hukumar sadarwa ta Uganda ta ce takaita kafafen sada zumunta na da nufin kare zaman lafiya da tsaron jama’a bayan zaben shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamnatin Uganda ta bayyana a ranar Lahadi cewa za ta ci gaba da dabbaka dokar hana amfani da kafafen sada zumunta na zamani a kasar.

Hakan na zuwa bayan dage katse hanyar sadarwar intanet da ta shafi kasa baki daya, sa’o’i kadan bayan sanar da Shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

An katse intanet ne kwanaki biyu kafin a bude rumfunan zabe da aka gudanar a ranar Alhamis, kamar yadda rahoton AFP ya bayyana.

Gwamnati ta ce ta dauki wannan mataki ne domin dakile yada “bayanan karya”, sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matakin a matsayin abin “damuwa matuka”.

Kara karanta wannan

Da gaske harkokin gwamnati sun tsaya cak a Kano Abba na shirin shiga APC?

An ci gaba da hana amfani da kafaen sada zumunta a Uganda
Ugandan President Museveni addresses some of his supporters at a rally in Bugiri | GettyImages (Stock)
Source: Getty Images

Meye ya faru bayan kada kuri’u a Uganda?

Ko da yake yawancin sassan kasar sun kasance cikin kwanciyar hankali bayan kammala zaben, an samu rahotannin kananan zanga-zanga a daren Asabar bayan fitar da sakamakon.

‘Yan jaridar AFP sun ce sun ji karar hayakin tarwatsa jama’a a wasu sassan babban birnin kasar, Kampala.

Da safiyar Lahadi, an lura cewa yawan jami’an tsaro a titunan Kampala ya ragu sosai, inda aka ga mutane suna zirga-zirga kamar yadda aka saba, tare da bude shaguna da kasuwanni.

Babban daraktan Hukumar Sadarwa ta Uganda (UCC), George Nyombi Thembo, ya ce har yanzu kafafen sada zumunta na zamani suna nan a kulle na wucin gadi.

Ya ce:

“Kafafen sada zumunta za su ci gaba da kasancewa a garkame domin kare kasar daga duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaron jama’a da zaman lafiya.”

Ba duka shafukan intanet a garkame ba

Kara karanta wannan

Alhaji Aliko Dangote ya yi kyautar sama da Naira biliyan 10

Thembo ya tabbatar da dawo da yawancin shafukan intanet, yana mai kare matakin dakatar da shi na tsawon kwanaki a matsayin “abu mai muhimmanci”.

Ya ce an dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar bayanan karya, bayanan bogi da kuma bayanan da aka kirkira da gangan domin yaudarar jama’a.

Ya kara da cewa an yi hakan ne domin dakile yiwuwar magudin zabe da kuma kare al’umma daga kiraye-kirayen tayar da tarzoma a irin lokacin mai matukar sarkakiya ga kasa.

Yaushe intanet zai zama kamar yadda yake a baya?

Sai dai ya ki bayyana lokacin da za a dawo da cikakken amfani da kafafen sada zumunta, yana mai cewa ba ya son sanya wani lokaci na hasashe.

Zaben Uganda dai ya gudana ne cikin tsauraran matakan tsaro da kuma karancin masu kada kuri’a.

Gwamnati ta dauki matakan ne domin hana barkewar zanga-zangar da za ta yi kama da wadda ta auku a kasar Tanzania mai makwabtaka da kasar a zaben da aka gudanar a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Masana harkokin siyasa sun dade suna kallon zabukan Uganda a matsayin abin da ake yi kawai domin cika ka’ida, ganin yadda Shugaba Museveni ke da cikakken iko kan harkokin gwamnati da jami’an tsaro na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

An gano gargadin da aka yi wa Donald Trump har Amurka ta fasa kai hari Iran

Yadda zaben Tanzania ya kasance

A wani labarin, an bayyana shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a matsayin wacca ta sake lashe zaben shugaban ƙasa da kusan kashi 98 na ƙuri’un da aka kada.

Samia Suluhu Hassan ta yi nasara ne duk da koke-koken da ke cewa an hana manyan ’yan adawa shiga zaben.

Al-Jazeera ta ce hukumar zaɓe ta ƙasa ce ta tabbatar da sakamakon a ranar Asabar, inda ta ce Hassan ta samu nasara a kusan dukkan mazabu na ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng