Kasar Uganda za ta fara amfani da tsarin kasuwancin musulunci

Kasar Uganda za ta fara amfani da tsarin kasuwancin musulunci

Ma'aikatar kudi ta kasar Uganda ta ce ta kammala shirye-shiryen fara amfani da tsarin kasuwanci na musulunci a bankunan kasar daga watan Octoban bana.

Mr Patrick Osailap wanda shine sakataren ma'ajin kasar ya ce kasar ta zabi tsarin lashes co addinin musuluncin ne don samawa yan kasar basusuka masu sauki.

"Majalisar kasar ta amince da dokar sai dai tana bukatan karin haske kan yadda za'a fara aiki dashi amma muna sa ran zuwa watan Oktoba za'a fara amfani dashi" inji Mr Ocailap.

Wata kasa zata karbi tsarin kasuwancin musulunci
Wata kasa zata karbi tsarin kasuwancin musulunci

KU KARANTA: Ai da ka dawo mana da kasafin kudin tunda baka amince da gyarar da mu kayi ba- Melaye ya fadawa Buhari

Ya kuma ce gwamnatin kasar za ta karbo bashin $20 miliyan daga bankin cigaban Afrika saboda yan Uganda su sami basusuka da za su habaka masana'antu da aikin noma.

Da a ka masa tambaya game da alkhairan da ke tattare da tsarin kasuwanci na musuluncin, Mr Fred Muhumza, kwarere a kan tattalin arziki ya ce, ba dole bane ya yi tasiri sosai kamar yadda ta faru a Kenya da Tanzania saboda an gina shi kan tsarin sharia'an musulunci.

"A maimakon a biyan kudin ruwa, ana raba riba ne ko akasin haka a kan bash on kuma kamar yadda ka sani mutanen mu ba su fiye bayyanawa ba idan sun sami riba," inji Mr Mahumza.

Sai dai Mr Jamil Ndyanga, Babban jami'in hulda da jama'a na Tropical Bank Limited, daya daga cikin bankunan da za su fara aiki da tsarin na kasuwancin musulunci ya ce ba gaskiya bane wai tsarin bai yi tasiri ba a Kenya.

Ya ce kawai wasu ne da basu fahimci tsarin ba ke yin irin wannan maganganun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel