Trump na Barazana ga Iran, Zanga Zanga Ta Barke a Amurka, ana Ta Arangama

Trump na Barazana ga Iran, Zanga Zanga Ta Barke a Amurka, ana Ta Arangama

  • Masu zanga-zanga da hukumomin Amurka sun sake fafatawa a Minneapolis sakamakon mutuwar wata mata da jami’in shige-da-fice ya harba
  • Dalibai a wasu makarantu sun bar azuzuwa suna nuna adawa da tsauraran matakan shige-da-ficen da gwamnatin Donald Trump ke aiwatarwa
  • Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin shugaba Trump ke cigaba da yi wa Iran barazanar kai farmaki game da zanga-zanga da ake yi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Tashin hankali ya kara tsananta a birnin Minneapolis na jihar Minnesota yayin da hukumomi da masu zanga-zanga suka sake gwabzawa a tituna, kwanaki bayan mutuwar Renee Good da aka harba yayin wani farmakin shige-da-fice.

Lamarin ya jawo tarzoma bayan harba barkonon tsohuwa sosai a unguwar da aka kashe Good, inda jama’a ke zargin jami’an tarayya da cin zarafi da tsoratarwa.

Kara karanta wannan

Halin da aka shiga bayan farmakar Hausawa a jihar Edo

Yadda ake zanga-zanga a Amurka
Hayaki ya tashi a filin zanga-zanga a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A lokaci guda, rahoton AP ya nuna cewa rikicin ya haifar da sabani a ofishin lauyan gwamnatin Amurka, inda wasu jami'ai suka yi murabus bisa ce-ce-ku-ce kan yadda ake binciken mutuwar.

Zanga-zanga ta yi kamari a Amurka

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Amurka sun yi amfani da barkonon tsohuwa da abubuwa masu sanya kaikayi a ido domin tarwatsa masu zanga-zanga yayin arangama.

Rahoton NBC ya bayyana cewa hayaki ya lullube tituna kusa da inda Renee Good ta mutu, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici sosai.

A wani gini, an ga wani mutum yana goge idanu da dusar kankara yana neman taimako bayan da jami’ai a cikin wata mota suka fesa masa wani sinadari mai launin ruwan dorawa.

Masu zanga-zangar kan rika busa sarewa, su yi ihu da tsokana a duk lokacin da suka hango jami’an shige-da-fice dauke da makamai suna wucewa cikin motoci marasa alama ko suna sintiri a tituna.

Kara karanta wannan

An sake kai hari kan Hausawa kusa da Uromi, an fatattake su bayan yanka awaki

Bayanin masu zanga-zanga a Amurka

Wata mazauniyar yankin da ake fafatawa, Brita Anderson, ta bayyana fushinta kan ganin jami’ai sanye da kayan yaki da abin rufe fuska.

Rahotanni sun nuna cewa ta ce hakan ya bata mata rai matuka, tana tambayar me ya kawo jami’an da irin wannan shiri zuwa cikin unguwar.

A wani bangare na jihar, dalibai a Brooklyn Park sun fice daga makarantu domin nuna adawa da matakan shige-da-ficen da ake aiwatarwa.

Daga bisani, taron jama’a mai yawa ya hallara a wajen wani otal a Minneapolis, inda suka rika buga ganguna da busa sarewa yayin da jami’an tsaro sanye da huluna da sanduna ke tsaye a bakin kofar.

Masu zanga zanga a Amurka
Masu zanga-zanga na fafatwa da jami'an tsaro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma, an samu arangama a wajen ginin gwamanati da ake amfani da shi a matsayin cibiyar ayyukan jami’an shige-da-fice a yankin Twin Cities.

Bayan harbin da ya kashe Renee Good, jami'ai biyar sun yi murabus daga ofishin lauyan gwamnatin Amurka, suna nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da binciken.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

Amurka ta yi gargadi kan Iran

A wani labarin, mun rahoto muku cewa gwamnatin Amurka ta yi gargadi ga dukkan kasashen duniya masu huldar kasuwanci da kasar Iran.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa zai lafta harajin kashi 25 ga duk wata kasa da ta cigaba da huldar kasuwanci da Tehran.

Trump ya ce matakin zai fara aiki nan take, kuma ya janye tattaunawa da zai yi da jami'an gwamnatin Iran kan cewa ana murkushe masu zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng