Yaki Ya Dauki Zafi: Rasha Ta Harba Makami Mai Karfin Nukiliya Ukraine
- Rasha ta yi amfani da makamin Oreshnik, wani makami mai linzami na zamani da ke tashi da gudu mai tsananin gaske, a hare-haren da ta kai kan wasu wurare a Ukraine
- Masana sun bayyana cewa Oreshnik na da karfin zuwa wurare da dama, abin da ke kara tsananta barazanar da yake haifarwa a wajen da aka harba shi
- Harin ya kara tayar da hankalin kasashen duniya, musamman ganin cewa an kai shi ne a yankin yammacin Ukraine da ke makwabtaka da kasashen da ke karkashin NATO
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Russia - Sabon mataki da Rasha ta dauka na amfani da makamin Oreshnik a yakin Ukraine ya sake jawo hankalin duniya kan irin makaman zamani da ake amfani da su a rikicin da ya shafe shekaru uku yana gudana.
Oreshnik, wanda sunansa ke nufin wani itace, na daga cikin makamai masu linzami masu matsakaicin zango da ke tafiya da gudu mai saurin gaske.

Source: Getty Images
New York Times ta wallafa cewa Rasha ta taba harba wannan makami a watan Nuwamban 2024, inda aka ce an yi amfani da shi domin gwaji.
Bayani kan makamin da Rasha ta harba
Oreshnik makami ne mai linzami da ke iya kai hari daga nesa, kuma yana tafiya da gudu fiye da na yawancin makaman da ake da su a yanzu.
An gina shi ne bisa tsarin RS-26 Rubezh, wanda tun da farko aka kirkiro shi a matsayin makami mai kai hari daga nahiyoyi zuwa nahiyoyi.
Daya daga cikin manyan siffofinsa shi ne tafiya mai nisa da daukar manyan makaman da za su iya kai hari wurare daban-daban a lokaci guda.
Wannan fasali yawanci ana danganta shi ne da manyan makaman ICBM, abin da ya sa Oreshnik ya zama na daban a makaman Rasha.
Makamin Oreshnik na da karfin nukiliya
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya taba bayyana cewa ba za a iya dakile makamin Oreshnik ba, kuma karfinsa na iya kai wa kusan na makamin nukiliya.
A karshen shekarar 2024, wasu jami’an Amurka sun nuna cewa kadan daga cikin irin wadandan makami ne kawai Rasha za ta iya mallaka.

Source: Getty Images
Reuters ta rahoto cewa duk da haka, tun daga 2024, Rasha ta fara samar da Oreshnik mai yawan gaske, tare da bai wa kawayenta na Belarus wasu daga ciki.
Sojojin Rasha sun ce harin da suka kai da Oreshnik martani ne ga yunkurin kai hari da jiragen sama marasa matuki da Ukraine ta yi kan wani gidan shugaban Rasha a yankin Novgorod a karshen shekarar 2025.
Amurka ta tare tankar man Rasha
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Amurka ta sanar da kama wani jirgin ruwa dauke tankar mai aka ce daga kasar Rasha ta fito.
Amurka ta ce ta kama tankar man ne saboda takunkumin da ta saka wa kasar Venezuela na hanata zirga-zirgar danyen mai zuwa kasashe.
A martanin da ta yi, gwamnatin kasar Rasha ta gargadi Amurka kan kama jirgin ruwan tare da kira ta gaggauta sakin wadanda ke tuka jirgin.
Asali: Legit.ng

