Mamdani: Musulmin da Ya Ci Zabe Ya Ruguza Shirin Isra'ila a Amurka
- Sabon magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya soke wasu dokokin da tsohon Magajin gari Eric Adams ya sanya masu alaƙa da kasar Isra’ila
- Gwamnatin Isra’ila ta zargi Mamdani da ƙara rura wutar kyamar Yahudawa bayan janye ma’anar IHRA kan nuna wariya da ya yi yana shiga ofis
- Mamdani ya mayar da hankali kan batun gidaje, inda ya bayar da umarni na gaggawa domin hanzarta gina gidaje a birnin domin saukaka rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Sabon magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya fara mulkinsa da matakai masu zafi bayan soke wasu muhimman dokokin da tsohon magajin gari, Eric Adams, ya sanya, musamman waɗanda suka shafi Isra’ila.
Rahoto ya nuna cewa Mamdani ya rattaba hannu kan sababbin dokokin ne a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan bikin rantsar da shi a City Hall.

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa matakin ya janyo muhawara mai zafi a cikin gida da waje, inda ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta fito fili ta zarge shi da rura wutar kyamar Yahudawa.
Zohran Mamdani ya kawo cikas ga Isra'ila
A cewar bayanai, Mamdani ya soke dukkan dokokin da Eric Adams ya kawo bayan 26, Satumba, 2024, ranar da aka gurfanar da Adams a gaban kotu.
Daga cikin dokokin da aka janye akwai wacce ta faɗaɗa ma’anar nuna kyamar Yahudawa, da kuma wacce ta hana ma’aikatan birnin da hukumominsa shiga adawar sayayya ko janye jarin kasuwanci daga Isra’ila.
Da yake magana da manema labarai, Mamdani ya ce ranar ta kasance wata alama ce da ta sa ’yan New York sake gamsuwa da shugabanci bayan da dama sun karaya a baya.
Korafin Isra'ila kan matakin Mamdani
Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta bayyana ɓacin ranta kan matakin Mamdani, inda ta ce sabon magajin birnin ya na kokarin ruruta wutar kyamar Yahudawa.
A wata sanarwa da ta wallafa a kafar X, ma’aikatar ta ce soke ma’anar IHRA da kuma cire takunkumin sayayya ba shugabanci ba ne.
Sai dai masu rajin kare haƙƙin Falasɗinawa sun yaba wa Mamdani, suna cewa matakin nasa ya nuna adalci da tsayawa kan ’yancin jama’a.
Al-Jazeera ta rahoto cewa sun bayyana cewa janye dokokin da suka fifita Isra’ila na daga cikin alkawuran da Zohran Mamdani ya yi yayin kamfen ɗinsa.
Mamdani ya fara aiki kan batun gidaje
Baya ga batun Isra’ila, Mamdani ya kuma rattaba hannu kan wasu dokokin da suka shafi matsalar gidaje, wadda ya yi ta jaddada muhimmancinsu tun lokacin yaƙin neman zaɓensa.
Dokokin sun umarci gwamnati da ta yi nazari kan yadda za a hanzarta gina gidaje, tare da tattara bayanan filayen gwamnati da za a iya amfani da su wajen gina gidaje.

Source: Facebook
An umurci hukumomi da su gabatar da cikakken rahoto a nan gaba kadan, domin a ɗauki matakan gaggawa kan matsalar gidaje da ke addabar birnin New York.
An rantsar da Mamdani da Kur'ani
A wani labarin, kun ji cewa sabon magajin garin New York, Zohran Mamdani ya sha rantsuwar fara aiki da Al-Kur'ani mai girma a Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karon farko da aka taba rantsar da magajin garin New York da Kur'ani a tarihin kasar.
Bayan kafa tarihin rantsuwa da Kur'ani, Mamdani ya kasance mutum na farko da ya ke da alaka da Afrika da ya zama magajin garin New York.
Asali: Legit.ng


