Trump na Zancen Kare Kirista, za a Yi Aiki da Kur'ani a Babban Birnin Amurka
- Zababben magajin birnin New York, Zohran Mamdani, zai kafa tarihi ta hanyar amfani da Alƙur’ani wajen rantsar da shi bayan lashe zabe
- Matashin ɗan siyasar zai zama Musulmi na farko da kuma ɗan Afirka na farko da aka taɓa zaɓa a wannan muƙami mai muhimmanci
- Rahotanni sun bayyana cewa zai sha rantsuwar ne da wani Alƙur’ani mai ɗauke da tarihin al’ummar Musulmi da baƙar fata a New York
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Zababben magajin birnin New York, Zohran Mamdani, zai kafa sabon tarihi a birnin yayin da zai yi rantsuwar kama aiki da Alƙur’ani mai tsarki, karo na farko da wani magajin birni zai yi haka tun kafuwar birnin.
An bayyana cewa Mamdani, mai shekaru 34, zai sha rantsuwar ne da dare a wata tsohuwar tashar jirgin ƙasa da ke ƙarƙashin ginin City Hall.

Source: Getty Images
Rahoton AP News ya ce zai zama Musulmi na farko, ɗan Asiya ta Kudu na farko, kuma ɗan Afirka da aka haifa a wajen Amurka na farko da ya riƙe muƙamin magajin birnin New York.
Mamdani zai rantse da Kur'ani a Amurka
Yawancin magabatan Mamdani sun yi rantsuwa ne da Bible, duk da cewa dokar rantsuwar ba ta tilasta amfani da wani littafin addini ba.
Sai dai Mamdani ya zaɓi Alƙur’ani domin nuna asalin sa da kuma girmama al’ummar Musulmi da suka mara masa baya a zaben da ya gabata.
Rahoton New York Times ya nuna cewa yayin yaƙin neman zaɓensa, Mamdani ya fi mayar da hankali kan batun tsadar rayuwa, amma bai ɓoye addininsa ba.
Ya rika ziyartar masallatai a sassa daban-daban na birnin, lamarin da ya taimaka wajen jawo goyon bayan sababbin masu kaɗa ƙuri’a daga al’ummar Musulmi da Asiya ta Kudu.
Alƙur’anai 3 da za a yi amfani da su
A rantsuwar farko da za a yi a tashar jirgin ƙasa, Mamdani zai ɗora hannunsa kan Alƙur’anai biyu, ɗaya mallakin kakansa, ɗaya kuma ƙarami wanda aka kiyasta an rubuta shi tun ƙarshen ƙarni na 18 ko farkon ƙarni na 19.
An bayyana cewa Kur'ani na biyun yana cikin tarin kayan tarihi na cibiyar Schomburg da ke ƙarƙashin ɗakin karatu na New York.
Mai kula da sashen Gabas ta Tsakiya da Nazarin Musulunci a cibiyar, Hiba Abid, ta ce Alƙur’anin yana wakiltar yaduwar Musulunci da haɗuwar al’adu a tarihin New York.

Source: Twitter
A rantsuwar da za a yi daga baya a City Hall a ranar farko ta shekarar 2026, Mamdani zai yi amfani da Alƙur’ani na kakansa da kuma kakarsa, kodayake ba a bayyana cikakken tarihinsu ba.
An yi gasar Kur'ani a Abujan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Izala mai hedqwata a Jos, jihar Filato ta kammala gasar karatun Al-Kur'ani a birnin tarayya Abuja.
Wani alaramma daga jihar Kaduna ne ya zama gwarzon shekara bayan fafatawa da aka yi tsakanin jihohin Najeriya baki daya.
Manyan mutane ne suka hallara wajen rufe gasar tare da raba kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara a matakai daban-daban.
Asali: Legit.ng


