Bayan Najeriya, Trump Ya Baro Rikici da Faransa da Kasashen Turai
- Shugabannin kasashe Turai sun zargi Amurka da matsin lamba da tsoratarwa bayan kakaba haramcin biza kan wasu fitattun mutanen su
- Rahotanni sun nuna cewa matakin da Amurka ta dauka ya shafi tsohon kwamishinan EU da wasu masu fafutukar yaki da yaɗa labaran ƙarya
- Hakan na zuwa ne yayin da rikicin ya kara zurfafa sabani tsakanin tarayyar Turai da gwamnatin Donald Trump kan dokokin fasahar zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Faransa – Rikici ya barke tsakanin Tarayyar Turai da Amurka bayan gwamnatin Washington ta kakaba haramcin biza kan wasu fitattun ’yan Turai da ke da hannu wajen kirkiro dokokin da ke sa ido kan manyan kamfanonin fasaha na Amurka.
Shugabannin Turai, ciki har da shugaban Faransa Emmanuel Macron, sun yi Allah-wadai da matakin, suna masu cewa yana nuni da tsoratarwa da kokarin murkushe ikon Turai kan harkokin fasahar zamani.

Source: Getty Images
The Guardian ta wallafa cewa wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar sabani tsakanin Turai da Amurka kan batun ’yancin faɗar albarkacin baki da dokokin da ke shafar kafafen sada zumunta.
Trump ya hana turawa shiga Amurka
Rahotanni sun nuna cewa haramcin bizar da Amurka ta kakaba ya shafi tsohon kwamishinan Tarayyar Turai kuma daya daga cikin masu tsara dokar fasahar zamani ta EU, Thierry Breton.
Sauran da abin ya shafa sun hada da Imran Ahmed daga Birtaniya, da Anna-Lena von Hodenberg da Josephine Ballon daga Jamus, da kuma Clare Melford.
Amurka ta bayyana cewa wadannan mutane na jagorantar yunkurin da ke matsa wa kamfanonin fasaha na Amurka su kakaba takunkumi kan ra’ayoyin da wasu ke adawa da su.
Martanin Amurka kan dokokin Turai
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce dokokin Turai na nufin tsoma baki ne a harkokin cikin gida na Amurka ta hanyar takaita ’yancin fadin albarkacin baki.
A cewarsa, gwamnatin Trump ba za ta amince da abin da ta kira “tsauraran matakan takaita ra’ayi” da ke shafar kamfanonin Amurka ba.
Martanin shugaban Faransa ga Amurka
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kakkausar suka a X kan haramcin bizar, yana mai cewa matakin na nufin cin zarafin Turai.
Ya jaddada cewa an amince da dokokin EU ta hanyar dimokuradiyya daga majalisar dokokin Turai da kasashen kungiyar.
Shugabannin Jamus, Spain, Birtaniya da jami’an EU sun goyi bayan Macron, suna cewa Tarayyar Turai na iya daukar matakin gaggawa idan har aka ci gaba da irin wadannan matakai.

Source: Facebook
Masana na ganin rikicin na iya zama wani sabon babi a takaddamar siyasa da al’adu tsakanin Turai da Amurka, musamman kan fasahar zamani.
Trump zai hana 'yan Najeriya zuwa Amurka
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald J Trump ya kafa dokar takaita shiga kasarsa da za ta shafi 'yan Najeriya.
A ranar 1 ga Janairun 2026 ne sabuwar dokar da Trump ya kawo za ta fara aiki a kan 'yan Najeriya da wasu kasashen duniya.
Gwamnatin Amurka karkashin Trump ta dauki matakin ne a wani shiri na hana baki shiga kasar domin inganta tsaron iyakoki.
Asali: Legit.ng

