Halin da ake ciki a Benin bayan Fatattakar Sojoji Masu Yunkurin Juyin Mulki

Halin da ake ciki a Benin bayan Fatattakar Sojoji Masu Yunkurin Juyin Mulki

  • Bayan sojoji sun mamaye gidan talabijin na ƙasar Benin tare da ikirarin kifar da shugaban ƙasa, sojojin gwamnati sun dakile yunkurin
  • Rundunonin Najeriya sun taimaka wajen tarwatsa masu yunkurin juyin mulkin, abin da ya dawo da natsuwa a manyan titunan Kotono
  • Rahoto ya nuna cewa mutane sun koma harkokinsu, duk da tsoro da ruɗanin da tankokin yaki da harin sama suka haddasa a kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Benin - Bayan yunƙurin juyin mulkin da ya girgiza Benin, hankula sun soma dawowa a birnin Kotono, cibiyar tattalin arziƙin ƙasar.

Mutane da dama sun taru wajen sayar da jarida na Chantal Dagah, alamar cewa jama’a na neman karin bayani kan abin da ya faru.

Wasu mutane a wani titon kasar Benin
Mutane na hada-hada a wani titin kasar Benin. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta rahoto cewa duk da tankokin yaki da aka gani a tituna da kuma harin sama da aka kai kan wasu wurare, birnin Kotono ya fara dawowa hayyacinsa.

Kara karanta wannan

Wasu manya a Kano sun ajiye Abba a gefe, sun ce Barau suke so a 2027

Jaridun cikin gida sun wallafa manyan kanun labarai na kwantar da hankali, inda aka yaba kalaman shugaban Patrice Talon game da tabbatar da zaman lafiya.

Halin da ake ciki a kasar Benin

A manyan titunan Kotono, musamman Boulevard de la Marina, jama’a sun soma komawa zirga-zirgar yau da kullum, musamman a titin na haɗa fadar shugaban ƙasa, filin jirgin sama, tashar ruwa da ma’aikatun gwamnati.

‘Yan kasuwa da masu sana’o’i sun koma bakin aikinsu. Masu adaidaita-sahu da ma’aikatan gwamnati suna kan hanyarsu kamar yadda suke a kowace rana.

Wani ma’aikacin ma’aikatar noma ya ce komai ya soma dawowa daidai, yana fatan kada a sake samun irin wannan tashin hankalin.

Wani matashi mai dinki, Thor, ya ce dolensa ya rufe shago saboda harin da aka kai kusa da sansanin sojoji da ke unguwarsu.

Ya ce ya koma bakin aiki don kauce wa asarar kuɗi, inda ya ce shagon nasa yana dab da sansanin da jiragen saman Najeriya suka kai wa hari a ranar yunƙurin juyin mulkin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Sojan da ya so jagorantar juyun mulki a Benin
Pascal Tigri da ya so kifar da gwamnatin Benin. Hoto: @fnicencool
Source: Twitter

A wani gidan cin abinci kusa da wurin, wasu kwastomomi suna tattaunawa kan ko rashin ciniki ya samo asali ne daga yunkurin juyin mulkin ko kuma ruwan sama mai tsanani da ke sauka a birnin.

An dauke tankokin yaki a kasar Benin

Rahoto ya ce an rage yawan tankokin yaki da aka gani a kasar, amma jama’a sun tabbatar da cewa ganin su a manyan tituna ya tayar da hankula.

Wasu jaridun ƙasar sun rahoto cewa bayanin shugaban Talon ya taimaka matuƙa wajen kwantar da hankalin al’umma.

Duk da cewa an samu ruɗani, makarantu sun buɗe, yara suna ketare manyan tituna cikin nutsuwa, yayin da masu sayar da kaya ke cigaba da kira ga kwastomomi domin farfado da kasuwanci.

Tashar A-Jazeera ta fitar da wani bidiyo game da yadda lamura suka fara daidaita a Benin bayan dakile yunkurin juyin mulki.

Pascal Tigri ya gudu Togo daga Benin

Kara karanta wannan

'Za a kamo shi,' Benin ta gano kasar da sojan da ya so juyin mulki ya buya

A wani labarin, kun ji cewa jagoran yunkurin juyin mulki a Benini, Laftanar Janar Pascal Tigri ya tsere zuwa kasar Togo.

Wani jami'in gwamnatin kasar ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce sun gano wajen da ya fake.

Gwamnatin Benin ta sanar da cewa za ta nemi Togo ta dawo mata da sojan domin ya fuskanci hukuncin da ya dace da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng