Nijar, Mali da Burkina Faso na Barazanar Harbo Jirage bayan Rike Jirgin Najeriya

Nijar, Mali da Burkina Faso na Barazanar Harbo Jirage bayan Rike Jirgin Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa kungiyar AES ta ba da umarni cewa a harbo duk wani jirgin da ya keta sararin samaniyar mambobinta
  • Umarnin ya biyo bayan zargin cewa jirgin saman sojojin Najeriya ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba
  • Shugaban kasar Mali, Asimi Goita ya ce shiga yankinsu ba tare da izini ba rashin mutuntawa ne ga dokokin ƙasa da ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kasashen Sahel ta AES da ta ƙunshi Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar, ta ba da umarni ga dukkan ƙasashe mambobinta su harbo jirgin da zai keta sararin samaniyar ƙungiyar ba tare da izini ba.

Wannan umarni ya fito ne bayan zargin da AES ta yi na cewa jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya shiga sararin saman Burkina Faso a ranar 8, Disamba, 2024.

Kara karanta wannan

Shugaban Burkina Faso Traoré ya rike sojojin Najeriya da jirginsu a kasar shi

Shugabannin kasashen AES
Shugabannin Mali, Nijar da Burkina Faso. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa AES ta ce jirgin, wanda ya ɗauki sojojin Najeriya 11, ya shiga sararin samaniyar ƙasar ba tare da izini ba, lamarin da ya tayar musu da hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan zargi ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sabanin siyasa da rikice-rikicen tsaro tsakanin ƙungiyar da sauran ƙasashen yankin, musamman bayan fitarsu daga ECOWAS.

Kasashen AES sun yi barazanar harbo jirage

A cikin wata sanarwa da shugaban Mali, Asimi Goita, ya sa wa hannu, AES ta bayyana cewa shugabannin ƙasasheta sun amince da saka dukkan tsarin kariyar sararin samaniyar ƙungiyar cikin shirin ko-ta-kwana.

Sanarwar ta nuna cewa tun daga 22, Disamba, 2024, shugabannin AES sun ba da izinin cewa duk jirgin da ya keta sararin yankin AES za a “kawar da shi nan take”, matakin da suka ce ya ƙara ɗaga darajar tsaron su.

Rahoton tashar Channels Television ya nuna cewa Goita ya bayyana keta sararin samaniya a matsayin karya dokokin ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan

ECOWAS ta tura zaratan sojoji Benin daga Najeriya da wasu kasashe 3

Ya ce yanzu shirye-shirye suna kan gaba domin tabbatar da cewa sararin saman ƙungiyar bai sake fuskantar irin wannan barazana ba.

Shugaban kasar Burkina Faso
Shugaban kasar Burkina Faso da ya tsare jirgin Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Batun jirgin Najeriya da ya je Benin

A ranar Lahadi rundunar sojin samann Najeriya ta bayyana cewa jirginta ya tashi zuwa jamhuriyar Benin domin taimakawa ƙasar wajen dakile masu kokarin juyin mulki.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya amince da buƙatun Benin guda biyu, ciki har da neman taimakon jirgin sama.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko jirgin ya shige yankin Burkina Faso ba yayin aikin, domin ƙasar na Arewa maso yammacin Benin ne.

A yanzu dai AES ta ce za ta ci gaba da kare sararin samaniyarta da dukkan ƙarfinta bayan zargin Najeriya ta keta mata doka.

Amurka ta yaba wa Najeriya kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar Amurka da ya zo Najeriya ya yaba da matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka.

Riley Moore ya yi magana ne bayan ganawa da mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Najeriya ta janye jirgin yakinta zuwa Benin bayan sanin halin da ake ciki

Dan majalisar ya bayyana cewa ceto daliban da aka yi a jihar Neja alama ce da ke nuna samun sauyi a tsarin tsaron Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng