'Yan Amurka Sun Shiga Tsaka Mai Wuya bayan Sabanin Trump da Majalisa
- Gwamnatin Amurka na kulle ba tare da aiki ba tun farkon Oktoban 2025, bayan majalisar dattawa ta kasa cimma matsaya kan kasafin kudi
- Fiye da ma’aikata 750,000 na gwamnati sun daina aiki, yayin da miliyoyin jama’a ke rasa tallafin abinci da inshorar lafiya a fadin kasar
- Tattaunawa tsakanin jam’iyyun Republican da Democrat ta ci tura, yayin da hakan ke cigaba da zama barazanar ga dubban Amurkawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Rikicin kulle gwamnati a Amurka ya wuce rana ta 40, bayan gazawar majalisar dattawan kasar wajen cimma matsaya kan batun kasafin kudi.
Wannan rikici ya haifar da dakatar da ma’aikatan gwamnati fiye da 750,000, tare da jinkirta tallafin abinci da kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen sama a duk fadin kasar.

Source: Facebook
Alj-Jazeera ta ce lamarin ya fara ne a ranar 1 ga Oktoban 2025, bayan jam’iyyar Republican ta ki amincewa da shirin Democrat na shirye-shiryen kiwon lafiya da tallafin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun daga lokacin, majalisar ta kasa amincewa da bukatun kudi 14 da za su ba da damar biyan albashi ga ma’aikata.
Bayan tsawon mako shida, jami’an jam’iyyun biyu na ci gaba da tattaunawa domin kawo karshen lamarin, amma har yanzu babu wata alamar da ke nuna za a cimma matsaya.
Barazanar karancin abinci a Amurka
Rahoton BBC ya nuna cewa Donald Trump ya bayyana cewa ba zai dawo da tallafin abinci ba sai an kawo karshen rufe gwamnatin.
Ya bayyana cewa shirin samar da tallafin abinci ga talakawa na kimanin Dala biliyan 8 a wata zai ci gaba da tsayawa har sai ‘yan Democrat sun bude gwamnati.
Shirin SNAP na taimaka wa talakawa da ba su da wadatar kudin abinci, inda mutum guda ke karbar kimanin Dala 190 a wata, yayin da iyalai ke samun kimanin dala 356.
Matsalar inshorar lafiya a Amurka
Yayin da rufe gwamnati ke cigaba, jam’iyyar Democrat na zargin Republican da kin sabunta tallafin inshorar lafiya na (ACA).
Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawa ta sake tsaya wa cak saboda Trump ya ki amincewa da tsawaita shirin.
Democrat na neman tsawaita wannan shiri na shekara guda domin taimaka wa wadanda ba su da inshorar aiki ko ta gwamnati su samu kariya.

Source: Getty Images
Trump ya yi jawabi yana cewa yana so a mayar da kudin inshora zuwa hannun ‘yan kasa kai tsaye domin su samu inshora mai inganci da kudinsu.
A halin yanzu, kusan mutane miliyan 24 ke cin gajiyar shirin ACA, kuma masana na gargadin cewa farashin inshora na iya ninkuwa nan da 2026 idan majalisar ta kasa tsawaita shirin.
Sojojin Amurka za su iya rasa albashi
Fiye da sojoji miliyan 1.3 na cikin hadarin rasa albashinsu, abin da zai iya matsa wa bangarorin biyu lamba su cimma matsaya.
Sai dai har yanzu babu tabbas ko gwamnatin za ta sake yin amfani da kudin binciken soji domin biyan albashi kamar yadda aka yi a baya.
Cikas a bangaren jiragen saman Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa rashin biyan albashi ga masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama ya haddasa karancin ma’aikata a fannonin tashi da saukar jirage.
A ranar Asabar da ta gabata, an soke tashin sama da jirage 1,530, yayin da aka da aka jinkirta tashin dubban jirage.
Yawan jiragen da aka soke tashinsu ya karu daga 1,025 a ranar Juma’a zuwa fiye da 1,500 a ranar Asabar, an jinkirta tashin fiye da 10,000 a ranar Lahadi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


