Donald Trump Ya Sa Sojojin Kasar Amurka Sun kai Hari Sun Kashe Mutane
- Sojojin Amurka sun kai sabon mummunan hari a wani jirgin ruwa a tekun Caribbean, wanda ya yi sanadin kashe mutane
- Pete Hegseth, ya ce an kai harin ne bisa umarnin Donald Trump kan jirgin da ake zargin ‘yan ta’adda ne ke tuka shi
- Majalisar dinkin duniya ta yi Allah-wadai da hare-haren tana kiran su kashe-kashen da ba su da hujja a dokar kasa da kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Sojojin Amurka sun sake kai wani mummunan hari a tekun Caribbean wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku.
Harin na zuwa ne bayan wasu hare hare da Amurka ta kai kan wasu jirage da sunan cewa 'yan ta'adda ne ke tuka su.

Source: Getty Images
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Ministan tsaron kasar, Pete Hegseth, ya tabbatar da kai harin a daren Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Donald Trump ya ce sojoji su kai hari
Hegseth ya ce harin ya kasance bisa umarnin shugaba Donald Trump, inda aka nufi wani jirgin ruwa da ake cewa na wata kungiya ce da Amurka ta ayyana a matsayin 'yar ta’adda.
Ya ce an kai harin ne a cikin ruwa, inda ya bayyana bidiyon da ke nuna lokacin da wani makami ya bugi jirgin kafin ya kama da wuta.
Amurka ta ce za ta cigaba da kai hari
Duk da cewa ba ta gabatar da hujja kai tsaye da ke nuna cewa jirgin na da hannu a fasa-kwaurin miyagun kwayoyi ba, Hegseth ya ce irin wadannan hare-hare za su ci gaba:
“Za su cigaba har sai ’yan ta’addan miyagun kwayoyi sun daina gurbata al’ummar Amurka.”
Ya kara da cewa:
“Ga duk wani da ke barazana ga kasarmu: idan kana son rayuwa, ka daina safarar miyagun kwayoyi. Amma idan ka ci gaba — za mu kashe ka.”
Hare-haren da Amurka ta kai a Satumba
Rahotanni sun nuna cewa tun farkon watan Satumba, fiye da mutane 60 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Amurka ta kai kan akalla jirage 18 a tekun Caribbean da kuma tekun Pacific.

Source: Getty Images
Sai dai babban jami’in kare hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya, Volker Turk, ya soki hare-haren, yana mai cewa:
“Babu hujjar kashe-kashen,”
‘Yan majalisar dokokin Amurka da dama na bukatar a bayyana hujjar doka da gwamnatin Trump ke amfani da ita wajen kai wadannan hare-hare a cikin ruwan duniya.
Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, ya zargi Trump da kokarin tayar da zaune tsaye a kasarsa ta hanyar wadannan hare-hare da kuma taruwar rundunar sojojin ruwa na Amurka a yankin.
Amurka na shirin kai hari Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Amurka sun fara tsara yadda za su kai hari Najeriya bayan zargin da Donald Trump ya yi.
Shugaban Amurka ya yi ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya kuma ba zai zuba ido ba.
Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta karyata zargin, Trump ya ce zai kai hari Najeriya domin kawo karshen 'yan ta'adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


