Saudiyya da kasashen Musulmi 7 na maraba da amincewar Hamas kan zaman lafiya da Isra'ila

Saudiyya da kasashen Musulmi 7 na maraba da amincewar Hamas kan zaman lafiya da Isra'ila

  • Donald Trump ya shiga tsakani domin samar da dauwamammen zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Hamas a wannan makon
  • Kasashen Larabawa sun bayyana jin dadi kan yunkurin Trump na kawo karshen rikicin Gaza mai dogon zamani
  • Rahoto ya bayyana bukatun da ake son cimmawa a wannan shiri na rage gallazawa Falasdinawa a yankinsu mai tarihi

Riyadh, Saudi Arabiya – Kasashe takwas na Larabawa da Musulmai sun bayyana jin daɗinsu kan yadda ƙungiyar Hamas ta amsa tayin zaman lafiya da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar don kawo karshen yakin Gaza.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa, ministocin harkokin wajen Saudi Arabiya, Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Indonesia, Pakistan, Turkiyya, Qatar da Masar sun bayyana maraba da matakan da Hamas ta dauka kan shirin shugaba Trump.

Yadda Trump ya shiga tsakani kan batun Gaza da Isra'ila
Hagu: Trump a zaman tattauna batun Gaza. Dama: Masu zanga-zanga kan lamarin Falasdinawa | Hotuna: Jim Lo Scalzo/EPA/Bloomberg da Chris McGrath
Source: Getty Images

Shirin dai ya bayyana nufin kawo karshen yakin Gaza, sakin duka wadanda ake tsare da su, da kuma fara tattaunawa nan da nan kan yadda za a aiwatar da Shirin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sa Isra'ila ta fara shirin tsagaita wuta kan Gaza

Trump ya kyauta, inji Larabawa

Ministocin sun kuma yaba da kira da Trump ya yi ga Isra’ila da ta dakatar da harin bama-bamai nan take, tare da fara aiwatar da yarjejeniyar musayar fursunoni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun nuna godiya bisa jajircewar shugaban wajen kokarin kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sun ce wadannan matakai na nuna wata babbar dama ce ta tsagaita wuta gaba daya, tare da magance matsalolin jin kai da al’ummar Gaza ke fuskanta.

Hamas sun yi dogon tunani, inji Larabawa

Hakazalika, ministocin sun yi maraba da sanarwar Hamas cewa tana shirye ta mika mulkin Gaza ga kwamitin rikon kwarya na Falasdinu wanda ya kunshi kwararru masu zaman kansu a fannin siyasa.

Sun jaddada muhimmancin fara tattaunawar cikin gaggawa don cimma matsaya kan yadda za a aiwatar da shirin cikin nasara.

Batun Isra'ila da Gaza: Abin da Larabawa suka ce kan Hamas
Shugaban Isra'ila da Trump a wurin tattauna tsagaita wuta | Hoto: Jim Lo Scalzo/EPA/Bloomberg
Source: Getty Images

Ministocin sun sake jaddada aniyarsu ta hadin kai wajen tallafawa aiwatar da shirin cikin gaggawa, tare da tabbatar da yarjejeniya mai cike da cikakkun manufofi da suka hada da kawo karshen yakin Gaza nan take, inji rahoton Saudi Gazette.

Kara karanta wannan

Ana shirin sulhu da Isra'ila, Sheikh Ahmad Gumi ya aika sako ga kungiyar Falasdinawa

Abubuwan da ake son cimmawa

Hakazalika da bayar da agajin jin kai ba tare da wata tangarda ba, hana kaura ko korar al’ummar Falasdinu daga kasarsu, tabbatar da tsaron dukkan fararen hula da saki dukkan wadanda ake garkuwa da su.

A bangare guda,shirin na nufin dawo da hukumar Falasdinu (Palestinian Authority) zuwa Gaza, hada Gaza da Yammacin Kogin Jordan da kuma kafa tsarin tsaro da zai kai ga cikakken janyewar sojojin Isra’ila daga Gaza da sake gina yankin.

A karshe, ministocin sun bayyana cewa wannan matakin zai bude sabon shafin zaman lafiya bisa tsarin kafa jihohi biyu, wanda zai tabbatar da adalci da kwanciyar hankali ga Falasdinu da Isra’ila.

Yakin Isra’ila da Falasdinu dai ba sabo bane, an shafe tsawon shekaru da nufin kawo karshen rikicin, amma har yanzu ba a cimma matsaya mai dorewa ba.

Tuni Isra'ila ta fara shiri

Kun ji cewa, rundunar sojin Isra’ila ta ce a ranar Asabar ta fara shirye-shiryen aiwatar da mataki na farko na shirin tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar domin kawo karshen rikicin Gaza, bayan Hamas ta nuna amincewa da wasu sassa na shirin.

Kara karanta wannan

Sharudan da Trump, Netanyahu suka gindaya domin tabbatar da zaman lafiya a Gaza

Rundunar ta bayyana cewa an ba ta umarni daga shugabannin kasar Isra’ila da ta fara “shirye-shiryen aiwatarwa” tare da mayar da aikinta zuwa na kariya kawai a cikin Gaza, duk da cewa ba a janye sojoji daga yankin ba.

Sanarwar ta zo ne bayan Trump ya umarci Isra’ila da ta dakatar da hare-hare da zarar Hamas ta nuna cewa ta amince da wasu muhimman sassa na shirin Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng