Donald Trump ya sa Isra'ila ta Fara Shirin Tsagaita Wuta Kan Gaza

Donald Trump ya sa Isra'ila ta Fara Shirin Tsagaita Wuta Kan Gaza

  • Isra’ila ta ce ta fara Shirin tsagaita wuta a yakin da take da Hamas bayan Sanya bakin da Donald Trump ya yi
  • Kungiyar Hamas ta amince da bukatun da Trump ya gabatar kan samar da zaman lafiya a yankin mai dogon tarihi
  • Kasashen duniya sun sha bayyana rashin jin dadinsu kan yadda Isra’ila ke sakin bama-bamai kan farare hula a Gaza

Tel Aviv, Isra’ila - Rundunar sojin Isra’ila ta ce a ranar Asabar ta fara shirye-shiryen aiwatar da mataki na farko na shirin tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar domin kawo karshen rikicin Gaza, bayan Hamas ta nuna amincewa da wasu sassa na shirin.

Rundunar ta bayyana cewa an ba ta umarni daga shugabannin kasar Isra’ila da ta fara “shirye-shiryen aiwatarwa” tare da mayar da aikinta zuwa na kariya kawai a cikin Gaza, duk da cewa ba a janye sojoji daga yankin ba.

Kara karanta wannan

Saudiyya da kasashen Musulmi 7 na maraba da amincewar Hamas kan zaman lafiya da Isra'ila

Tsagaita wuta a Gaza zai ba da tasirin zaman lafiya
Lokacin da Donald Trump ya gana da shugaban Isra'ila a kan batun Gaza | Hoto: Jim Lo Scalzo/EPA/Bloomberg
Source: Getty Images

Sanarwar ta zo ne bayan Trump ya umarci Isra’ila da ta dakatar da hare-hare da zarar Hamas ta nuna cewa ta amince da wasu muhimman sassa na shirin Amurka.

A cewar Trump:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina ganin sun shirya don samun zaman lafiya mai ɗorewa.”

Manufar kiran da Trump ya yi

Ya fadi shirin nasa ne a matsayin dama ta karshe don kawo karshen yakin da ya dauki kusan shekaru biyu tare da tabbatar da sakin wadanda ake garkuwa da su.

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya nuna goyon bayansa ga shirin daga birnin Washington, kamar yadda Saudi Gazette ta bayyana.

Wani babban jami’in Masar ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa don sakin fursunoni da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Falasdinu, inda daruruwan Falasdinawa ke cikin jerin waɗanda za a saki.

Haka kuma ana tattauna batun hada kan kungiyoyin Falasdinu don tsara makomar Gaza tare da samar da mafitar dindindin.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

Adadin mutanen da Gaza ta rasa a yaki

Kungiyar Palestinian Islamic Jihad, wadda ta yi watsi da shirin a baya, a ranar Asabar ta ce yanzu tana goyon bayan amsar da Hamas ta bayar.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasu a rikicin ya haura 67,000, inda mata da yara suka kai kusan rabin wadanda suka mutu.

Shugaban kasar Isra'ila a wurin taro
Shugaban Isra'ila lokacin da yake magana a Washington DC kan batun Gaza | Hoto: Alex Wong
Source: Getty Images

Rahoton ya ce wadannan alkaluma an tabbatar da su ne ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma an kara sabbin sunaye fiye da 700 a cikin rajistar rashin.

Hamas za ta saki Isra’ilawa

Shirin Trump ya tanadi cewa Hamas za ta saki mutane 48 daga cikin Isra’ilawan da take tsare cikin kwanaki uku, tare da mika makamai da kuma mika ikon mulkin Gaza ga wasu Falasdinawa.

A gefe guda kuma, Isra’ila za ta dakatar da farmaki, ta janye dakarunta, ta saki fursunoni, tare da ba da damar shigar kayayyakin agajin jin kai shiga yankin da kuma sake gina zirin Gaza.

Kara karanta wannan

Ana shirin sulhu da Isra'ila, Sheikh Ahmad Gumi ya aika sako ga kungiyar Falasdinawa

Hamas ta amince da sakin wadanda take tsare da su da kuma mika ikon mulkin, amma har yanzu ba ta yarda da shirin ajiyar makamai ba, wanda shi ne babban abin da ke haifar da cikas.

A gefe guda kuma, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Barcelona da wasu manyan biranen Turai suna neman kawo karshen yakin.

Hanzari ba gudu ba...

A Gaza, mazauna yankin irin su Samir Abdel-Hady sun nuna shakku da cewa:

“Abin da muke so shi ne a aiwatar da abin da aka ce da gaske… muna so mu ga zaman lafiya a kasa.”

Iyayen Isra’ilawan da ake tsare da su sun bayyana fatan ganin ‘ya’yansu, inda Yehuda Cohen, wanda dansa ke tsare a Gaza yace:

“Mun mika amana a hannun Trump, domin shi kafai ne yake kokarin kawo mafita."

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng