FBI Ta Sa Ganimar $10,000 kan Dan Najeriya da Ake Zargi da Sata a Bankin Amurka

FBI Ta Sa Ganimar $10,000 kan Dan Najeriya da Ake Zargi da Sata a Bankin Amurka

  • Wani 'dan asalin Najeriga ya ballo aiki a kasar Amurka bayan an zarge shi da laifin yin satar kudade
  • Hukumar binciken manyan laifuffuka ta kasar Amurka (FBI), ta sanya ganima kan duk wanda ya ba ta bayanan da za su kai ga cafke wanda ake zargin
  • Wanda ake zargin dai ya cika wandonsa da iska ne kafin a fara shari'arsa, inda tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Amurka - Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka (FBI) ta sanya ladan Dala 10,000 a neman da take yi wa wani dan asalin Najeriya.

Hukumar FBI ta sanya kudin ne ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Olumide Adebiyi Adediran, ɗan asalin Najeriya mai shekara 56.

FBI na neman dan Najeriya ruwa a jallo
Hoton shugaban hukumar FBI, Kash Patel da wasu jami'ai Hoto: @FBI, @FBIDirectorKash
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar FBI ta sanya a shafin X a ranar Laraba, 24 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama malamim addinin musulunci a jihar Bauchi

Meyasa ake neman dan Najeriya a Amurka?

Ana neman Olumide Adebiyi Adediran ne saboda zargin yin damfara ta banki a Amurka.

A cewar FBI, Adediran ya yi amfani da bayanan sata na ‘yan kasar Amurka wajen buɗe asusun banki da kuma asusun cire kuɗi.

A sanarwar, hukumar FBI ta ce wanda ake nema ya shiga wani banki a Champaign, jihar Illinois, inda ya yi kokarin cire kuɗi daga wani asusu.

FBI ta ce Adediran ya tsere daga jihar Illinois a karshen watan Disamba, 2001, jim kaɗan kafin a fara shari’arsa kan zarge-zargen damfara ta banki, damfarar bayanan karya da kuma damfara ta katin cire kudi.

Daga bisani, a ranar 2 ga Janairu, 2002, kotu bayar da sammacin kama shi saboda karya sharuɗɗan belinsa.

Wane bayani hukumar FBI ta yi?

"Ana neman Olumide Adebiyi Adediran bisa karya sharuɗɗan belinsa. A watan Agusta, 2001, ya shiga banki a Champaign, Illinois, inda ya yi kokarin cire kuɗi daga asusun ajiya na banki."

Kara karanta wannan

Trump ya yi wa shugabannin Iran da suka shiga Amurka rashin mutunci

"Haka kuma, ana zargin ya yi amfani da bayanan sata na na ‘yan ƙasar Amurka wajen buɗe asusun banki da cire kuɗi."
"Adediran ya tsere daga yankin 'Central District of Illinois' a karshen watan Disamba, 2001, kafin fara shari’arsa a kan laifuffukan damfara da ake zarginsa da su."
"An bayar da takardar sammacin kama shi a ranar 2 ga Janairu, 2002, bayan tuhumarsa da karya sharuɗɗan belinsa."

- FBI

FBI na neman dan Najeriya a Amurka
Hoton 'dan Najeriyan da hukumar FBI ke nema Hoto: @FBIMostWanted
Source: Twitter

Hukumar ta bukaci duk wanda ke da bayani game da wanda ake nema da ya tuntubi ofishin FBI mafi kusa da shi, ko kuma ya kai rahoto ga ofishin jakadancin Amurka mafi kusa.

FBI ta cafke wanda ya shirya hari kan sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar FBI ta samu nasarar cafke wanda ya shirya hari kan sojojin Najeriya a jihar Borno.

Hukumar FBI ta cafke Anas Sa'id wanda ake zargi da kitsa hari kan shingen binciken sojoji a shekarar 2023.

FBI ta bayyana cewa an cafke Anas ne a birnin Houston, Texas, yayin da ake zarginsa da shirin kai wani sabon hari na ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng