Khamenei Ya Yi Bayani bayan Gama Yaki da Isra'ila, Ya Gargadi Trump da Netanyahu
- Shugaban Iran, Ali Khamenei, ya bayyana cewa Isra’ila ta kusa rushewa kafin Amurka ta shiga yakin da aka yi tsakanin kasashen biyu
- Ayatollah Khamenei ya ce harin da Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka babbar nasara ce da za a iya maimaitawa idan an sake kawo mata hari
- Shugaban ya jaddada cewa Iran ba za ta taba mika wuya ga Amurka ba, yana mai cewa burin kasar shi ne ganin sun mika wuya gaba ɗaya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - A karo na farko tun bayan ƙarshen rikicin mako biyu tsakanin Iran da Isra’ila, Ayatollah Ali Khamenei ya yi jawabi ga al’umma.
Ali Khamenei ya bayyana cewa Isra’ila ta kusa rushewa gaba ɗaya sakamakon hare-haren da Iran ta kai mata.

Kara karanta wannan
Bayan yaƙi da Isra'ila, Shugaba Trump ya faɗi abin da Amurka za ta tunkari Iran da shi

Source: Getty Images
Legit ta gano bayanin da shugaban ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Khamenei ya ce da Amurka ba ta shiga yakin ba, da yanzu da Isra’ila ta zama kufai, yana mai cewa Amurka ta shiga yakin ne domin ta kare abokiyar kawancenta.
A cewar Khamenei:
“Mun ci nasara a kan Amurka. Ta shiga yakin ne domin tana ganin Isra’ila za ta rushe idan ba ta shiga ba, amma babu abin da ta cimma.”
Iran ta ce hare-haren ta sun yi nasara
Ayatollah Khamenei ya bayyana harin da Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya a matsayin wani muhimmin abu.
Ya ce hakan wata shaida ce ta ƙarfin Iran da kuma ƙarancin ikon Amurka da kawayenta wajen hana Iran kare kanta.
Aljazeera ta wallafa cewa ya ce:
“A kowane lokaci da aka kai hari kan Iran, za mu maimaita irin wannan martani mai tsanani,”
Khamenei ya bayyana cewa kai wa manyan sansanonin sojin Amurka hari abu ne da Iran ke alfahari da shi.
“Ba za mu mika wuya ba” – Khamenei
Shugaban na Iran ya yi watsi da kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, inda ya ce Trump ya bayyana cewa Iran na bukatar mika wuya.
Khamenei ya ce hakan ba zai yiwu ba domin Iran ƙasa ce mai ƙarfi da za ta ci gaba da kare kanta daga duk wani yunkuri na tilasta mata.
Ya ce:
“Amurka za ta ci gaba da kira mu mika wuya, amma hakan ba zai taba faruwa ba. Wannan ƙasa ta Iran ƙasa ce mai ƙarfi,”
Isra’ila ta kusa rushewa inji Khamenei
Khamenei ya jaddada cewa Isra’ila ta fuskanci mummunan hari daga Iran wanda ya kusa halaka tsarin tsaron ƙasar.
Ya ce Iran ta yi amfani da makaman da suka girgiza tsarin soja da fasahar Isra’ila, lamarin da ya jefa Tel Aviv cikin matsanancin yanayi.

Source: Twitter
Iran ta halarci taro a China bayan yaki
A wani rahoton, kun ji cewa ministocin tsaron Iran da Rasha sun yi wani taro na musamman a kasar China.
Kasar China da ta jagorancin taron ta koka kan yadda ake cigaba da samun rikice rikice a fadin duniya.
Wasu rahotanni sun nuna cewa an tattauna batutuwan da suka shafi yaki da Iran da Isra'ila suka shafe kwana 12 suna gwabzawa.
Asali: Legit.ng

