Cikin Kunya Isra'ila Ta Fadi Asarar da Iran Ta Jawo Mata a Yakin Kwana 12

Cikin Kunya Isra'ila Ta Fadi Asarar da Iran Ta Jawo Mata a Yakin Kwana 12

  • Bayan kammala yaki, hukumomin Isra’ila sun ce mutane 28 sun mutu a hare-haren Iran, yawancinsu fararen hula
  • Baya ga haka, Isra'ila ta sanar da cewa fiye da mutane 3,000 ne suka jikkata, yayin da gidaje 31,000 da motoci 4,000 suka lalace
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa kasar Iran ta harba makamai masu linzami da rokoki kusan 1,550 zuwa Isra'ila cikin kwanaki 12

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Israel - Hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa hare-haren da Iran ta kai kan ƙasarsu cikin kwanaki 12 sun yi sanadin mutuwar mutane 28.

Baya ga haka, hare haren sun yi sanadiyyar jikkatar fiye da mutane 3,000 a Isra'ila wanda mafi yawansu fararen hula ne.

Israila ta fadi hasarar da aka mata a yaki da Iran
Israila ta fadi hasarar da aka mata a yaki da Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan barnar da aka yi wa Isra'ila ne cikin wani rahoto da Kuwait Times ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Trump ya yi tonon silili a taron NATO, ya ce Isra'ila ta sha wuta a hannun Iran

Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce an kwantar da mutane 3,238 a asibitoci sakamakon hare-haren, inda wasu 23 suka samu munanan raunuka yayin da wasu 111 ke da kananan raunuka.

Wannan tashin hankali na zuwa ne bayan Iran ta kaddamar da abin da hukumomin Isra’ila suka bayyana a matsayin hari mafi girma da aka kai kan ƙasarsu daga waje.

Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi amfani da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka.

An fadi barnar da Iran ta yi wa Isra'ila

Dakarun Isra’ila (IDF) sun ce Iran ta harba kimanin makamai 550 masu linzami da wasu jiragen yaki marasa matuka 1,000 zuwa ƙasar a cikin mako biyu da suka gabata.

A cewar IDF, akalla makamai 31 daga cikin waɗanda aka harba sun faɗi ne a cikin birane ko kuma wuraren da ke da muhimmanci.

Daga cikin wuraren da harin ya shafa akwai tashar wutar lantarki a Kudancin Isra’ila, wani kamfanin tace mai a Haifa da kuma wata jami’a a tsakiyar ƙasar.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi yawan mutane da ta rasa da masu raunuka bayan yaki da Isra'ila

Wani rahoto da CNN ta fitar ya bayyana cewa hare-haren sun lalata gine-gine kusan 31,000 da kuma motoci kusan 4,000 a faɗin ƙasar.

Halin da aka shiga a Isra'ila bayan harin Iran

A cikin waɗanda suka jikkata, kimanin mutane 138 sun kamu da matsanancin firgici, lamarin da ke nuna tasirin hare-haren ga lafiyar kwakwalwar jama’a.

Haka nan, hukumomin lafiya sun ce akwai mutane 30 da har yanzu ba a tantance irin raunukan da suka samu ba.

Israila na cigaba ta tattara barnar da Iran ta mata
Israila na cigaba ta tattara barnar da Iran ta mata. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Yayin da Isra’ila ke ƙoƙarin farfado da ababen more rayuwa da suka lalace, akwai fargabar cewa hare-haren na Iran na iya haifar da gagarumin koma baya ga tattalin arzikin ƙasar.

Donald Trump bai rusa nukiliyar Iran ba

A wani labarin, kun ji cewa wani rahoton sirri da aka samu ya karyata ikirarin shugaban Amurka na rusa cibiyoyin nukiliyar Iran.

Bayan wani hari da ya kai Iran a makon da ya wuce, Donald Trump ya ce ya samu nasarar rusa cibiyar nukiliyar Iran baki daya.

Sai dai fitar rahoton ya nuna shakku kan batun Trump, duk da cewa fadar White House ta ce an fitar da rahoton ne domin kunyata shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng