Kasar Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa kan Duba Watan Sallar Azumi
- Kotun Kolin Saudiyya ta bukaci Musulmi da ke kasar da su duba jinjirin watan Shawwal a daren Asabar 29 ga Ramadan 1446AH
- Duk wanda ya hango watan da ido ko ta amfani da na'urorin zamani ya na da damar sanar da kotu mafi kusa domin tabbatarwa
- An samu sabon tarihin yawan masu ibada a Masallacin Harami, inda suka kai sama da mutum miliyan 3.4 a daren 27 ga Ramadan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Kotun Kolin Saudiyya ta bukaci dukkan Musulmin da ke kasar da su duba jinjirin watan Shawwal a daren Asabar 29 ga Ramadan 1446AH, wanda ya yi daidai da 29 ga Maris, 2025.
Duba watan yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da karshen watan Ramadan da kuma sanar da ranar bikin idin sallar azumi.

Asali: Facebook
A cikin sanarwar da kasar ta fitar a shafinta na Facebook, an bukaci duk wanda ya hango wata da ido ko da na’urar hangen wata da ya kai rahoto zuwa kotu mafi kusa domin tabbatar wa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan mataki na daya daga cikin hanyoyin da ake bi domin tabbatar da ganin wata yadda ya dace da dokokin Musulunci.
Duba watan Shawwal don sanar da Idi
Ana sa ran bayan an duba wata, hukumomin Saudiyya za su sanar da hukuncin karshe na ko za a yi Sallar Idi a ranar Lahadi ko kuma a ranar Litinin.
Duba watan Shawwal yana daya daga cikin muhimman al’amuran da ke tabbatar da karshen azumin Ramadan.
A kowace shekara, hukumomin Saudiyya kan bukaci Musulmi su duba jinjirin wata domin tabbatar da ranar da za a gudanar da sallah bayan kammala azumi.
A kan samu mutane da dama da ke kokarin hango watan daga yankuna daban-daban na kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan
Za a share hawayen ƴan Najeriya, Majalisa ta ɗauki mataki kan tsadar datar MTN da Airtel
Bayan samun rahotanni daga shaidu masu inganci, kotun koli za ta yanke hukunci na karshe wanda zai bayyana ranar Sallah.
Masallacin Harami ya kafa sabon tarihi a Saudi
A wani rahoto daban, an bayyana cewa a daren 27 ga Ramadan, Masallacin Harami da ke birnin Makka ya karbi fiye da mutum miliyan 3.4 da suka gudanar da ibada da aikin Umrah.
Hakan ya nuna an kafa sabon tarihi na yawan jama’a da suka taru a Harami a lokaci guda a watan Ramadan.

Asali: Twitter
Ma'aikatar Harkokin Addini ta Saudiyya ta bayyana cewa shirin da suka tsara don gudanar da ibada a daren 27 ya samu cikakken nasara.
An tabbatar da tsaro da jin dadin masu ibada da suka hallara domin neman rahamar Allah a cikin daren.
Sheikh Budair ya jagoranci sallah a Madinah
A daren 27 ga Ramadan, Sheikh Budair ya kasance daya daga cikin limaman da suka jagoranci sallar dare a Masallacin Annabi da ke birnin Madinah.
Jama’a daga sassa daban-daban na duniya sun hallara domin yin ibada a wannan dare na 27 da ake sa ran ya kasance daren Lailatul Qadri.
An yi hasashen ganin watan sallah
A wani rahoton, kun ji cewa wani mai ilimin taurari ya yi hasashen cewa za a haifi jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar mai zuwa.
Rahoton Legit ya nuna cewa mai hasashen ya bayyana yanayin sararin samaniya da zai iya jawo ganin watan ko akasin haka idan ya fito.
Asali: Legit.ng