Shugaban Soji a Najeriya zai Jagoranci Rundunar Sojojin Saman Afrika
- Shugaban Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Hasan Abubakar, ya karɓi shugabancin Ƙungiyar Hafsoshin Sojin Sama na Afirka (AAAF).
- Hasan Abubakar ya jaddada bukatar haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen Afirka domin yaki da ta’addanci, ‘yan tawaye da miyagun laifuffuka
- Biyo bayan samun shugabancin, Najeriya za ta karɓi bakuncin taron sojojin saman Afrika a shekarar 2026 kuma wani taron a Mayun 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, CAS Hasan Abubakar, ya karɓi shugabancin Ƙungiyar Hafsoshin Sojin Sama na Afirka ta AAAF.
Legit ta gano hakan ne bayan nada Hassan Abubakar a lokacin taron sojojin saman Afrika da aka gudanar a Zambia daga 16 zuwa 22 ga Fabrairu 2025.

Asali: Facebook
Rundunar sojin saman Najeriya ta wallafa a X cewa za a gudanar wasu taruka na musamman a nan gaba kadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin jawabinsa, Hassan Abubakar ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da sauran ƙasashen duniya zai taimaka wajen inganta tsaro da kuma dakile barazanar ‘yan ta’adda.
An bukaci hadin gwiwa a Afrika
Abubakar Hassan ya ce haɗin gwiwa tsakanin rundunonin sojin saman ƙasashen Afirka zai taimaka wajen inganta dabarun yaki da ta’addanci da kare yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban sojin saman ya ce:
“Haɗin kai da kyakkyawan tsarin aiki tare tsakanin ƙasashen Afirka ne kawai zai iya kawo mafita kan matsalolin tsaro da muke fuskanta.”
Haka zalika, ya jaddada cewa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya zai bai wa ƙasashen Afirka damar habaka fasahar sarrafa jiragen yaki, dabarun yaki a sararin samaniya.
Shugaban sojojin ya kara da cewa hadin gwiwar za ta kuma jawo kyautata ayyukan agaji ga waɗanda suka shiga ibtila’i.
Najeriya za ta karbi bakuncin sojojin Afrika
A yayin taron, Abubakar Hassan ya tabbatar da cewa Najeriya za ta karɓi bakuncin taron hafsun sojojin saman Afrika a shekarar 2026.
Bugu da ƙari, Najeriya za ta karɓi wani taron sojojin sama karo na huɗu a birnin Lagos daga 21 zuwa 23 ga Mayu 2025.
An bayyana cewa hakan na nuna irin gagarumar gudunmawar da rundunar sojin saman Najeriya ke bayarwa wajen ci gaban tsaro a Afirka.

Asali: Facebook
Ana sa ran manyan hafsoshin soji daga sassa daban-daban na duniya da masana tsaro za su hallara domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen inganta tsaro ta amfani da fasahar zamani.
Bayan sanarwar karɓar shugabancin AAAF, mutane da dama sun yi ta taya Hasan Abubakar murna bisa wannan gagarumar nasara.

Kara karanta wannan
Karya ta kare: Sojoji sun gano maboyar Bello Turji, sun fadi lokacin kawar da shi
An soki matakin Amurka kan tsaron Afrika
A wani rahoton, kun ji cewa an saki matakin da sojin Amurka suka dauka na shiga yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Afrika.
Wata kungiyar zaman lafiya a Najeriya ta yi Allah wadai da matakin inda ta ce ba lallai ya haifar da zaman kafiya a Afrika ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng