Arzikin Dangote Ya Timbatsa, Ya Samu Sabon Matsayi cikin Masu Kudin Duniya

Arzikin Dangote Ya Timbatsa, Ya Samu Sabon Matsayi cikin Masu Kudin Duniya

  • Aliko Dangote ya zama mutum na 86 mafi arziki a duniya bayan dukiyar sa ta karu da kusan kashi 100% zuwa Dala biliyan 23.9
  • An ruwaito cewa babban hannun jarinsa a matatarsa ne ya kara masa daraja, inda a baya yana matsayi na 144 da Dala biliyan 13.4
  • Dangote ya yi nisa ga attajiran Afirka irinsu Johann Rupert na Afirka ta Kudu da Mike Adenuga na Najeriya a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya sake hawa matakin manyan masu kudi a duniya bayan dukiyarsa ta ninka zuwa Dala biliyan 23.9.

Lamarin ya sa Dangote ya dawo cikin jerin attajirai 100 mafi arziki a duniya, matsayi da bai kai ba tun shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Trump zai binciki zargin tallafawa Boko Haram daga Amurka

Dangote
Dangote ya dawo mutum na 86 cikin masu kudin duniya. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Business Day ta wallafa cewa Dangote ne ke jagorantar jerin attajiran Afirka, inda ya yi zarra da nisa kan sauran ‘yan kasuwa irinsu Johann Rupert da Mike Adenuga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya ingiza tattalin Dangote sama?

Babban dalilin da ya sa arzikin Dangote ya haura haka shi ne mallakar kashi 92.3% na matatar mansa da ke jihar Legas.

Matatar ta kakkabe tsarin sayen man fetur daga waje da gwamnatin Najeriya ke yi tsawon shekaru masu yawa.

Ginin matatar na daya daga cikin manyan ayyukan masana’antu a duniya kuma ya shafe shekaru 11 yana gina ta, inda ya kashe Dala biliyan 23.

A cewar Forbes, matatar na iya tace gangar danyen mai 650,000 a rana, wanda ya sa ta zama mafi girma a Afirka da ta bakwai mafi girma a duniya.

Tasirin matatar Dangote a duniya

Tun bayan da matatar Dangote ta fara aiki a bara, an samu raguwar shigo da man fetur Najeriya, wanda ya sauya tsarin cinikin man fetur na Turai da ke dogaro da kasuwar Najeriya.

Kara karanta wannan

Adamawa: 'Yan ta'adda sun kai hari babban asibiti, an yi awon gaba da bayin Allah

Rahoton kamfanin Vortexa ya nuna cewa shigo da man fetur Najeriya ya ragu zuwa mafi karancin mataki cikin shekaru takwas, sakamakon matatar Dangote.

Haka nan, rahoton S&P Global ya tabbatar da cewa Najeriya ta fara fitar da man jirgin sama zuwa kasashen duniya, wanda ke nuna sauyin tattalin arzikin kasar.

Dangote na sauya fasalin tattalin Najeriya

Aliko Dangote ya bayyana cewa manufarsa ita ce sauya Najeriya daga kasa mai dogaro da danyen mai zuwa kasa da ke tace mai da kanta da fitar da shi zuwa kasashen waje.

A cewarsa, matatar za ta yi gasa da masana’antun Turai wajen samar da man fetur ga ‘yan Najeriya, wanda zai rage dogaro da kasashen waje.

Wata masaniyar tattali a Afrika, Zainab Usman ta ce yawancin ‘yan Najeriya na kallon Dangote a matsayin gwarzo da ke kawo cigaba.

A cewarta:

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi kalubalen 'karayar arziki' da ya fuskanta yayin gina matatar mai

“Yawancin mutane a Najeriya na kallon Dangote a matsayin wani gwarzo kuma babban dan kasuwa da ke gina masana’antu da canza kasar.”

Fadi tashi wajen gina matatar Dangote

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi bayani kan gwagwarmayar da ya yi wajen gina matatar mai a Legas.

Dangote ya ce ya sha fama ta bangarori da dama wanda da an yi nasarar dakile shi da ta shi ta kare a harkar kasuwanci a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel