Tchiani: An Fara Hana 'Yan Najeriya Shiga Kasar Nijar da Fasfon Ecowas

Tchiani: An Fara Hana 'Yan Najeriya Shiga Kasar Nijar da Fasfon Ecowas

  • Jamhuriyar Nijar ta fara hana ‘yan Najeriya masu fasfon ECOWAS shiga kasarta, sai dai idan suna da fasfo na kasa da kasa
  • ‘Yan kasuwa da matafiya sun koka kan yadda jami’an tsaron Nijar ke amfani da wannan doka wajen karbar cin hanci daga matafiya
  • Duk da wannan mataki, har yanzu iyakar Illela da Konni na bude, amma ana zargin cewa Nijar na shirin hana babura wucewa tsakanin kasashen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin hana ‘yan Najeriya da ke amfani da fasfon ECOWAS shiga kasarta ba tare da fasfo na kasa da kasa ba.

Wannan na zuwa ne bayan ficewar kasar daga kungiyar ECOWAS tare da Mali da Burkina Faso, lamarin da ke kawo sauye-sauye a dokokin shige da fice tsakanin kasashen yankin.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Tinubu
'Yan Najeriya sun koka kan shiga Nijar da fasfon ECOWAS. Hoto: Bayo Onanuga|Zagazola Makama
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa iyakar Illela (Najeriya) da Konni (Nijar) na ci gaba da kasancewa a bude, amma ana fuskantar matsaloli masu nasaba da shigar da sababbin dokokin shige da fice.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasuwa sun koka kan matsalar

Wasu ‘yan kasuwa da ke safara tsakanin Najeriya da Nijar sun koka kan yadda jami’an tsaron Nijar ke hana masu amfani da fasfon ECOWAS wucewa.

Wani dan kasuwa da ke yawan shiga da fita tsakanin kasashen biyu, Alhaji Mansur Abdullah, ya ce an fara kokarin kawar da fasfon ECOWAS a matsayin wata hanya ta tafiye-tafiye.

Sahara Reporters ta rahoto cewa Alhaji Mansur Abdullah ya ce:

“Sun fara takura mana idan muna nufi shiga kasar. Wasu daga cikinmu har an mayar da su gida saboda ba su da sabon fasfon da ake bukata.”

A cewarsa, wasu ‘yan kasuwar sun fara tsoron irin tasirin da wannan mataki zai yi kan harkokinsu na kasuwanci.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba da aka kama tulin makamai ana yunƙurin shigo da su Najeriya

Zargin karbar cin hanci wajen matafiya

Wasu matafiya sun bayyana yadda jami’an tsaron Nijar ke amfani da wannan sabon tsari wajen karbar kudi daga matafiya.

Wani direban mota da ke zirga-zirga daga Illela zuwa Konni, Abubakar Isa, ya bayyana cewa jami’an tsaron Nijar na karbar CFA5,000 zuwa 10,000 wajen masu fasfon ECOWAS.

Abubakar Isa ya ce:

“Idan ka zo iyakar, za su dauke ka zuwa ofishinsu su bukaci fasfo, wanda sun san ba mu da shi. Sai su bukaci mu biya cin hanci kafin mu wuce.”

Matukin motar ya kara da cewa wasu daga cikin matafiya da ba su da kudin cin hanci ana mayar da su gida.

Ana cigaba da zuwa kasuwanci Nijar

Duk da wannan sabon tsari, wasu ‘yan kasuwa sun bayyana cewa har yanzu ba a samu wani canji a harkokin kasuwanci ba.

Wani dan kasuwa a Illela, Alhaji Nuhu Abubakar, ya ce har yanzu iyakar na bude, kuma mutane na ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan

Manyan sarakuna 5 masu daraja da kotu ta tsige daga sarauta a cikin shekara 1

Nuhu Abubakar ya ce:

“Mun ji jita-jitar cewa gwamnatin mulkin soja ta Nijar na shirin hana babura shiga da fita tsakanin kasashen biyu, amma har yanzu babu wani takamammen mataki da aka dauka.”

Sai dai wasu matafiya na fargabar cewa lamarin na iya kara tsanani a nan gaba, musamman idan gwamnatin Nijar ta kakabawa masu fasfo na ECOWAS dokar hana shiga kai tsaye.

Martanin ECOWAS kan lamarin

Har yanzu gwamnatin Nijar ba ta fitar da wata takardar hukuma da ke tabbatar da doka ta hana fasfon ECOWAS ba.

A wata tattaunawa da aka yi da shugaban sashen yada labarai na ECOWAS, Joel Ahofodji, a ranar Litinin, ya bayyana cewa kungiyar ba ta da wata masaniya kan matakin da Nijar ta dauka.

Nijar ta zargi Najeriya kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa alakar Nijar da Najeriya na cigaba da dagulewa kan zargin makarkashiya.

Ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare ya zargi Najeriya da hada kai da wasu kasashen duniya domin kawo mata cikas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng