Daga Karshe Isra'ila da Hamas Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta, Bayanai Sun Fito
- An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a faɗan da ake yi Zirin Gaza tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan ƙungiyar Hamas
- Cimma yarjejeniyar tsagaita wutar na zuwa ne bayan an kwashe watanni 15 ana faɗa wanda ya jawo rasa rayuka masu yawa
- Hukumar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 46,000 waɗanda mafi yawansu fararen hula ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Gaza, Falasɗinu - An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta don kawo ƙarshen watanni 15 da aka kwashe ana gwabza faɗa a Zirin Gaza.
Faɗan dai an gwabza shi ne a tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan ƙungiyar Hamas mai fafutukar ƙwatar ƴancin Falasɗinawa.
Jaridar NBC News ta ce jami'an Hamas da Isra'ila masu masaniya kan tattaunawar, sun tabbatar da cimma yarjejeniyar a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cimma yarjejeniya tsakanin Hamas da Isra'ila
Wannan yarjejeniya mai wahalar cimmawa za ta sanya a sako mutane da dama da ake garkuwa da su a Gaza, tare da sako Falasdinawa da ke gidajen yari na Isra'ila.
Tsagaitar wutar ita ce ta biyu bayan yarjejeniyar daina faɗa da aka cimma ta mako ɗaya wacce ta ƙare a ranar 1 ga watan Disamba, 2023.
Wannan labarin ya biyo bayan makonni ana tattaunawa wacce ƙasashen Amurka, Qatar da Masar suka jagoranta, cewar rahoton BBC.
Isra’ila da Hamas ba su sanar da wannan yarjejeniya ba a hukumance, duk da cewa wani babban jami’in Hamas, Basem Naim, ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta amince da ita.
“Muna farin cikin cimma yarjejeniya a yau don dakatar da farmakin da ake yi wa mutanenmu, amma abin takaici shi ne za mu iya cimma wannan yarjejeniya tun a watan Mayun bara."
- Basem Naim
Wata majiya da ke da masaniya ta kai tsaye kan tattaunawar da wani jami’in Isra’ila da aka shaidawa batun yarjejeniyar, su ma sun tabbatar da labarin.
Shugaba Joe Biden zai yi magana kan yarjejeniyar
Ana sa ran Shugaba Joe Biden zai yi jawabi kan yarjejeniyar daga bisani a ranar Laraba.
Tun da farko, wata majiya mai alaƙa da diplomasiyya a Washington ta bayyana cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na shirin ganawa da majalisar tsaro, inda ake sa ran za a amince da yarjejeniyar cikin sauri.
Bayan haka zai miƙa yarjejeniyar ga cikakkiyar majalisar ministoci, wacce ita ma ake sa ran za ta amince.
Ana sa ran rukunin farko na waɗanda aka yi garkuwa da su za su fito ranar Lahadi, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa a Gaza
Isra'ila ta ƙaddamar da farmakin soja a Zirin Gaza bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda Isra'ila ta ce an kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da wasu mutum 250.
Sama da mutum 100 aka sako a ƙarshen watan Nuwamban 2023 yayin da aka dakatar da rikicin na ɗan lokaci, inda aka saki fursunoni 240 na Falasdinawa a madadinsu.
Yaƙin ya yi sanadiyyar lalata kusan dukkanin ababen more rayuwa na Zirin Gaza, tare da raba mutanen yankin da matsugunansu.
Hukumar lafiya a Gaza ta ce sama da Falasdinawa 46,000 ne sojojin Isra'ila suka kashe waɗanda mafi yawansu fararen hula ne.
Amurka ta buƙaci Isra'ila ta tsagaita wuta a Gaza
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Amurka ta buƙaci Isra'ila ta kawo ƙarshen yaƙin da take yi a Zirin Gaza na Falasɗinu.
Sakataren gwamnatin Amurka, Anthony Blinken ne ya yi wannan kiran, ya nuna cewa Isra'ila ta cimma dukkanin abubuwan da take buƙata a Gaza.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng