"Mu na Gyara," Facbook, WhatsApp Sun Dawo Aiki bayan Samun Matsala a Fadin Duniya
- Kamfanin META ya shaidawa jama'a cewa bai ji daɗin halin da su ka shiga a yammacin Laraba ba
- Mahajojin kamfanin da su ka haɗa da Facebook, WhatsApp da Instagram sun samu ƴar tangarɗa
- Sai dai kamfanin ya cika alƙawarin da ya yi na cewa za su gyara matsalar da aka samu a cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar America - A yammacin Laraba ne manyan manhajojin sada zumunta guda biyu mallakin kamfanin META su ka samu matsala.
Mutane a sassan duniya daban-daban sun koka saboda gaza amfani da kafofin yadda aka saba, inda matsalar Facebook ta fi ƙamari a wasu yankunan.
A saƙon da kamfanin META ya wallafa a shafin X, ya yi martani a kan dalilan samun matsalolin, tare da shaida wa masu amfani da zaurorin halin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Facebook, WhatsApp sun daina aiki
Jaridar The Cable ta ruwaito META ya ce ya na sane da matsalolin da masu amfani da manhajar Facebook da WhatsApp da Instagram su ka shiga fadin duniya.
Kamfanin ya nemi jama'a su ƙara haƙuri, yayin da aka kai 90% na gyare-gyaren da ake yi domin tabbatar da sun ci gaba da aiki yadda aka saba.
WhatsApp da Facebook sun dawo aiki
Tun a yammacin Laraba aka tabbatar wa da masu amfani da dandalin WhatsApp cewa komai zai sautu bayan ƙanƙanin lokaci.
WhatsApp ta wallafa cewa;
" Mu na sane da ƙalubalen da ake fuskanta wajen amfani da WhatsApp. Mu na aiki tuƙuru domin saita komai, mun lura wasu sun fara shiga manhajar ba tare da matsala ba. Mu na sa ran komai zai daidaita nan ba da jima wa ba."
An yi kutse a manhajar WhatsApp din gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ƴan dambara sun jefa gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno a cikin damuwa bayan sun yi nasarar kutsawa manhajarsa ta WhatsApp.
Rahotanni sun ce ƴan damfarar yanar gizo da ake kira da ƴan Yahoo sun riƙa bin mutanen da gwamnan ke mu'amala da su tare da neman rancen kuɗi tare da alkawarin biya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng