An Bayyana Ɓangarorin da Saudiyya za Ta yi Haɗaka da Najeriya

An Bayyana Ɓangarorin da Saudiyya za Ta yi Haɗaka da Najeriya

  • A ranar Litinin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya,, Muhammad bin Salman
  • A yayin wata tattaunawa da suka yi, gwamnatin Saudiyya ta yi alkawarin cigaba da tallafawa tattalin Najeriya musamman a harkar noma
  • Daga cikin ribar da Najeriya ke tsammanin samu akwai wata haɗaka da ake shirin kullawa da Saudiyya a kan sha'anin kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Gwamnatin tarayya ta fitar da rahoto kan ganawar Bola Tinubu da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya.

A ranar Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya gana da Muhammad bin Salman a wani shiri na haɗaka kan harkokin tattalin arziki.

Saudiyya
Saudiyya za ta yi hadaka da Najeriya. Hoto: Federal Ministry of Information and National Orientation, Nigeria
Asali: Twitter

Ma'aikatar yada labaran Najeriya ce ta wallafa yadda zaman Bola Tinubu da Yarima Muhammad bin Salman ya kasance a kafar Facebook.

Kara karanta wannan

Abin da Yariman Saudiyya ya faɗawa Bola Tinubu kan cire tallafin mai da wasu tsare tsare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadakar kasuwancin Najeriya da Saudiyya

Bayan ganawar Tinubu da Muhammad bin Salman, kasashen sun tattauna kan yadda za su kulla alaƙar kasuwanci a harkar albarkatun man fetur.

Tattaunawar ta kai ga samar da kwamitin kasuwanci da zai hada kasashen biyu domin kawo cigaba a tsakaninsu.

A karkashin haka, Yarima Muhammad bin Salman ya yabawa Bola Tinubu game da kokarin da yake yi na farfaɗo da tattalin Najeriya.

An bukaci Saudiyya ta zuba jari a Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta bukaci kasar Saudiyya ta zuba jarin $5b a wasu harkokin kasuwanci.

A shekarar 2022 kamfanin noma da kiwo na kasar Saudiyya (SALIC) ya zuba jarin $1.24b a kamfanin noman Najeriya na Olam.

Kasar Saudiyya za ta tallafawa Najeriya

Yayin da yake jawabi, Yarima Muhammad bin Salman ya bayyana cewa a shirye yake domin yin haɗaka da Najeriya.

Yarima Muhammad bin Salman ya tabbatar da cewa zai ba jami'an gwamnati umarnin tattaunawa kan duba bangarorin da suka dace su yi haɗaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun ji ruwan alburusai, sun fara guduwa daga Najeriya

Tinubu ya bukaci yancin Falasdinawa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya mika wasu manyan bukatu a taron kasashen Larabawa da Musulmi a Saudiyya.

Daga cikin bukatun da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar akwai dakatar da yakin da kasar Isra'ila ke kai wa kan Falasdinawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng