Hezbollah Ta Yi Ruwan Rokoki kan Sansanin Sojojin Isra'ila
- Kungiyar Hezbollah ta kai harin manyan rokoki a Arewacin Isra'ila inda ta ragargaza maboyar makamai a yankunan Dishon da Dalton
- Da take tabbatar da harin, Isra'ila ta ce rokoki 194 Hezbollah ta wulla cikin kasarta, amma ba ta fadi irin barnar da aka yi mata ba
- Hezbollah ta kara da cewa ta kai wani harin manyan rokoku yankin Yir'on da aka tabbatar matattarar 'makiya' kuma an yi barna a Tel Aviv
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Lebanon - Da alama kungiyar fafutuka ta Hezbollah ta gaji da yadda Isra'ila ke taka ta wajen kai hare-hare Lebanon da sauran wuraren da ke da alaka da ita.
A daren Lahadi ne kungiyar ta harba manyan rokoki kan ma'ajiyar makaman Isra'ila da ke Arewacin kasar inda aka yi gagarumar barna.
BBC ta wallafa cewa kungiyar Hezbollah ta kai hari kan wurin ajiyar makaman Isra'ila a daren Talata wayewar Laraba a yankin Dishon da Dalton.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hezbollah ta kai hari kan Isra'ila
United News of India ta wallafa cewa mayakan Hezbollah sun harba rokoki kan Arewacin Isra'ila inda ake da yakinin su na ajiye makamansu.
Haka kuma kungiyar ta tabbatar da kai hari kan wani wuri da ta bayyana a matsayin matattarar makiya a yankin Yir'on da ke iyaka da Lebanon.
Hezbollah ta harba rokoki 190 a Isra'ila
Mayakan Hezbollah sun ce akwai wasu hare hare da ta kai kan sansanin sojin Isra'ila da ke dab da Tel Aviv, kamar yadda ta tabbatar a ranar Litinin.
Haka kuma ta ce a harin, kasar Isra'ila ta bayyatar da cewa Hezbolla ta harba mata manyan rokoki guda 190 cikin kasarta.
Hezbollah ta ragargaji sojojin Isra'ila
A baya kun ji cewa kasar Iran ta ji zafin kisan shugaban kungiyar Hezbollah, Hasssan Nasrallah a harin da su ka kai Lebanon, inda sojojinta su ka ragargaji dakarun Isra'ila a harin ramuwar gayya.
Lamarin ya ja hankalin duniya inda aka fara hasashen tarihi zai iya maimaita kansa inda aka gwabza kazamin yaki tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hezbollah a shekarar 2006.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng