Isra'ila Ta Sake Tsokano Fada a Yankin Gabas Ta Tsakiya

Isra'ila Ta Sake Tsokano Fada a Yankin Gabas Ta Tsakiya

  • Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta kai wani hari a yankin Arewacin zirin Gaza a ci gaba da kai hare-haren da take yi
  • Harin da IDF ta kai ya yi sanadiyyar kashe shugaban gwamnatin Hamas a zirin Gaza, Rawdhi Mushtaha da wasunsa
  • Ƙungiyar Hamas ba ta ce komai ba dangane da harin wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutanenta guda uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Gaza, Falasɗinu - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shugaban gwamnatin Hamas a zirin Gaza.

Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta bayyana cewa ta kashe Rawhi Mushtaha, wanda shi ne shugaban gwamnatin Hamas a Gaza.

Isra'ila ta kashe shugaban Hamas
Isra'ila ta kashe shugaban gwamnatin Hamas a Gaza Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Wannan harin na nuni da yadda rikicin Isra’ila da Falasɗinu ke ci gaba da ruruwa.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu," Kwankwaso ya bayyana jam'iyyar da ta yunƙuro da ƙarfinta a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra'ila ta kashe shugaban gwamnatin Hamas

Jaridar Sky News ta rahoto cewa rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta tabbatar da kashe wasu manyan shugabannin Hamas guda uku.

Cikin wadanda sojojin kasar Isra'ilan suka hallaka har da Rawdhi Mushtaha.

Yadda aka kashe Rawdhi Mushtaha a Gaza

Da take ba da cikakken bayani kan harin da ya hallaka shugabannin Hamas guda uku, IDF ta ce an kai harin ne a wani gini da ke ƙarƙashin ƙasa a Arewacin Zirin Gaza.

IDF ta bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar kashe Rawhi Mushtaha da wasu kwamandojin Hamas guda biyu, Sameh Siraj da Sameh Oudeh.

Ƙungiyar Hamas ba ta ce komai ba dangane da harin zuwa lokacin tattara rahoton nan.

Adadin mutanen da suka mutu a Gaza ya ƙaru a cikin ƴan kwanakin da suka gabata bayan hare-haren Isra'ila ke ci gaba da kaiwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan roƙon ƙasar China ta yafewa Najeriya bashi

Wanene Rawdhi Mushtaha?

An haifi Rawdhi Mushtaha a shekarar 1959 a unguwar Shuja'iyya da ke a zirin Gaza.

An kama shi ne a shekarar 1988, watanni kaɗan bayan aurensa, kuma ya shafe kusan shekaru 25 a gidan yari.

Rawdhi Mushtaha yana da hannu wajen kafa rundunar tsaron (ISF) da aka fi sani da al-Majd, wacce ita ce ƙungiyar leƙen asiri ta Hamas da ke aiki a ƙarƙashin ma'aikatar cikin gida.

Iran ta kai hari kan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kai zafafan hare haren ramuwar gayya kan ƙasar Isra'ila a ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi nufin wargaza wasu wuraren sojin Isra'ila ne yayin kai hare haren da makamai masu linzami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng