Saurayinta Ya Cinna Mata Wuta, 'Yar Wasa Ta Mutu Tana Budurwa

Saurayinta Ya Cinna Mata Wuta, 'Yar Wasa Ta Mutu Tana Budurwa

  • Shahararriyar yar wasan Olympics a kasar Uganda ta rigamu gidan gaskiya bayan saurayinta ya cinna mata wuta
  • Budurwar mai suna Rebecca Cheptegei ta rasu ne kwanaki hudu bayan saurayinta ya kunna mata wuta kamar yadda aka tabbatar
  • Hukumar wasan Olympics a kasar Uganda ta yi Allah wadai da harin inda ta ce saurayin ya jawo babbar asara a kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Uganda - Kasar Uganda ta yi babban rashi bayan yar wasan Olympics da saurayinta ya ƙona ta rigamu gidan gaskiya.

Rahotanni sun nuna cewa Rebecca Cheptegei ta rasu ne kwanaki hudu bayan harin da ake zargi saurayinta ya kai mata.

Kara karanta wannan

Gini mai hawa 2 ya rikito a Kano bayan mamakon ruwa, mutane sun kwanta dama

Rebecca
An kona yar wasan Olympics. Hoto: @drukare
Asali: Twitter

Jami'in Olympics na kasar Uganda, Donald Rukare ne ya sanar da mutuwar Rebecca Cheptegei a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uganda: Yadda saurayi ya kona budurwa

Rahoton yan sanda ya nuna cewa wani saurayi mai suna Dickson Ndiema ake zargi da cinnawa Rebecca wuta.

Yan sanda sun bayyana cewa an zargi saurayin ne da watsawa Rebecca man fetur da kuma cinna mata wuta a ranar Lahadi da ta wuce.

Punch ta wallafa cewa Rebecca Cheptegei ta samu kuna sosai inda sama da kashi 80% na jikinta ya samu mummunan rauni.

Budurwa 'yar wasan Olympics ta rasu

Babban asibitin MTRH a kasar Uganda ya sanar da mutuwar Rebecca Cheptegei a ranar Laraba bayan jinyar kwanaki hudu da ta yi.

Jami'in wasan Olympics a kasar Uganda, Donald Rukare ya yi Allah wadai da abin da aka yi wa Rebecca Cheptegei inda ya ce lamarin ya yi muni sosai.

Kara karanta wannan

Yadda ake zargin yunwa na kashe fursunoni a gidajen yarin Najeriya

Rebecca Cheptegei ta fafata a gasar Olympics da aka kammala a birnin Faris a watan Agusta da ya wuce inda ta zo ta 44 a gasar tsere.

Ese ta yi aron keke a wasan Olympics

A wani rahoton, kun ji cewa yar Najeriya da ta yi gasar tseren keke a rukunin wasannin Olympics ta bayyana halin da ta shiga yayin da ta rasa keke.

Ese Ekpeseraye da ta wakilci Najeriya a gasar tseren keke na duniya a 2024 ta ce ta karbi aron keke ne domin shiga gasar saboda kasarta ba tayi mata tanadi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng